Sarauniya Batulu Hammangabdo: Darussan da sarauta ta koya mini
Hajiya Batulu Hammangabdo Muhammad ita ce Sarauniyar Gashaka da ke Jihar Taraba, ta yi Kwamishinar Ruwa a Jihar Taraba, sannan ita ce mace ta farko da ta rike mukamin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Taraba. Ta yi aikin jarida inda ta rike mukamin Daraktar Tsare-tsare da Bincike da Nazari a Hukumar Watsa Labarai ta Jihar Taraba. Ta […]
Hajiya Batulu Hammangabdo Muhammad ita ce Sarauniyar Gashaka da ke Jihar Taraba, ta yi Kwamishinar Ruwa a Jihar Taraba, sannan ita ce mace ta farko da ta rike mukamin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Taraba. Ta yi aikin jarida inda ta rike mukamin Daraktar Tsare-tsare da Bincike da Nazari a Hukumar Watsa Labarai ta Jihar Taraba. Ta bukaci mata su mayar da hankali wajen neman ilimi.
Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Hajiya Batulu Hammangabdo Muhammad, ni ’yar Lamidon Gashaka da ke Jihar Taraba, Alhaji Hammangabdo ce. Na fara makarantar firamare ta Central a Gashaka a shekarar 1973, daga baya na koma wurin kawuna da ke Maiduguri, wato marigayi Idris Waziri, inda na ci gaba da karatu, bayan an yi masa canji wurin aiki zuwa Yola, a Jihar Adamawa ne sai na na shiga Sakandaren Gwamnati da ke Fufure. Bayan na kammala sai na fara makarantar gaba da sakandare a College of Preliminary Studies da ke Yola.
Daga nan sai na yi digiri a aikin jarida a Jami’ar Maiduguri, inda na yi hidimar kasa a gidan talabijin na Gongola, wanda yanzu ake kiransa Gidan talabijin na Adamawa, a matsayin mai gabatarwa ta 2, daga baya aka dauke ni aiki, haka na ci gaba da aiki har na zama shugabar sashin shirye-shirye na gidan talabijin din. Na yi aiki da gidan talabijin din har zuwa shekarar 2000 da Gwamnan Jihar Taraba na lokacin Jolly Nyame ya nada ni Kwamishinar Ruwa, a wa’adin zangonsa na biyu ne ya nada ni mace ta farko da ta rike mukamin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Taraba. Na rike wannan mukamin tsawon shekara biyu, har zuwa lokacin da ya yi wa mukarrabansa garambawul.
Daga nan na ce ya dace in ci gaba da aikin jarida, hakan ya sanya na koma aiki da Hukumar Watsa Labarai ta Jihar Taraba, inda na rike mukamai masu yawa har zuwa Daraktan Tsare-tsare da Nazari da kuma Bincike, inda 2013 Mukaddashin Gwamnan Jihar Taraba Alhaji Garba Umar ya nada ni Kwamishinar Mata da Bunkasa Karkara. A kwanakin baya kuma aka nada ni Sarauniyar Gashaka.
Abubuwan da ba zan manta da su ba
Ina tuna lokacin da nake tare da mahaifana a Gashaka, ni da abokaina mukan je bakin kogi, wani lokaci mukan wurin don biki ne; wani lokaci kuma don yawo kawai. Haka idan dare ya yi, farin wata ya fito mukan yi rawar zabbe inda makada kan yi mana kida da ganguna muna rawa, saboda da haka nake tsayawa a wurin kakata, domin idan ina gida mahaifina ba zai bar ni in fita ba, a kullum ina tuna wadannan abubuwa. Lokacin da na koma wurin kawuna kuma sai rayuwata ta sauya, domin na koma rayuwar mutanen birni.
Halayen da na koya a wurin iyayena
Na fi daukar halayen mahaifina, mutum ne mai jan mutane a jiki da kuma haba-haba. Yana da hakuri, amma idan aka kure shi, ba ya yi wa mutum da dadi, nima haka nake.
Burina ina karama
Tun ina karama nake so in zama ’yar jarida, nakan tuna lokacin da nake tare da kawuna a Maiduguri, idan lokacin labaran karfe 9 na dare ya yi, nakan zauna a kusa da shi, nakan mayar da hankalina gaba daya don in kalli labaran, nakan lura da duk yadda mai karanta labarin yake yi, nakan fada wa kaina wata rana zan zama kamarsa, burina ya cika, ina gode wa Allah SWT.
Farin cikin zama uwa
Na samu ’yata na farko ne a lokacin da nake hidimar kasa, na sha wahala domin sai da aka yi mini tiyata, a lokacin ba ni da karfin da zan iya daukarta har sai bayan wata daya, duk da haka na yi farin cikin zama uwa.
Alhamdullillah, a yau duk ’ya’yana sun girma. Babu abin farin ciki kamar a ce yau ka haihu. ’Ya’yana su ne abokaina, ina yi musu addu’ar Allah Ya albakarci rayuwarsu.
Yadda na hadu da mijina
Mijina a lokacin shi ne shugaban makarantar sakandare a garinmu, yana da aboki wanda shi kuma shugaban makarantar firamare ne, shi yake aure antina, wata rana sai ya je ya ziyarce su, a nan ya ga hotona a cikin kundin adana hotunansu, don haka sai ya tambayi sunana da kuma wurin da nake, suka fada masa ina wurin kawuna a Maiduguri, daga nan ya ce sai ya je wurin da nake.
Wata rana na je hutu garinmu sai mutane suka rika kira na da matar Firinsifal, abin ya rika ba ni mamaki, daga baya ne antina ta sanar da ni halin da ake ciki. Daga nan ya je neman izini wurin iyayena. A lokacin ina karama don haka ba na son aure, na fi so in ci gaba da karatu, ya yi hakuri sosai, shi ne ya yi mini rijistar makarantar gaba da sakandare, inda na samu maki 9, wanda hakan ya ba ni damar shiga Jami’ar Maiduguri, daga nan ne ya ce ya kamata mu yi maganar aure sosai, amma sai kawuna ya ce sai na kammala digirina, amma ina shekara ta uku a jami’a na fada wa iyayena su sanya ranar aurena, daga nan aka yi mini aure, na so mijina sosai, mutum ne mai hakuri, mun haifi ’ya’ya 3, Rakiya da Idris Waziri da kuma Maryam. Har zuwa shekarar 2002 da Allah Ya yi mini rasuwa sakamakon hadarin mota a kan hanyarsa ta zuwa Gombe.
Yadda nake tunawa da mijina
Nakan tuna irin soyayyar da ya nuna mini, yana damuwa da dukkan abubuwan da suka shafe ni. Ina tuna lokacin da nake matsayin mai gabatarwa a gidan talabijin na Adamawa, mukan kammala aiki ne cikin dare, ban cika zama a gida ko da ranakun hutun karshen mako ba, idan lokacin girkina ya yi, kasancewar ina da kishiyoyi, amma duk da haka zan dawo a makare in girka masa shinkafa jalof, hakan ya sanya ya fara kira na ‘Batulu Jalof’, duk lokacin da aka biya ni albashi, sai in ware lokacin na musamman don in yi masa girke-girke na musamman. A kullum na tuna nakan yi hawaye, domin ya yi hakuri da ni.
Mutanen da nake koyi da su
Ina koyi da Annabi Muhammadu (SAW) da kuma ’yarsa Fatima, wadda ake kiran ta Batulu. Na gode Allah, ina fata in kasance kamar ita.
Ado da Kwalliya
Ina son sanya tufafin da zai dace da Musulma, wata tufafin da zai rufe mini jikina, ya kare ni daga bayyana tsiraici, sannan ina so in rika sanya tufafi mai launi daya.
Yadda nake hutawa
A kullum nakan so in rika karanta al-kur’ani, hakan yakan ba ni natsuwa da kwanciyar hankali, yakan kara mini kusaci da Allah. Nakan kwaikwayi yadda Sheikh Abdulrahman Yola yake yi. Na biyu nakan yi hira tare da ’ya’yana, a nan nakan fahimci halin da suke ciki, da kuma abin da suke so su yi.
Yadda nake motsa jiki
Ba na samun lokacin da nake motsa jiki, amma zan yi kokai in samu lokacin da zan rika yi, yana da amfani ga lafiyar jiki.
Nasarori
Babbar nasarar da na samu ita ce, ina zaune da jama’a lafiya, ina sanya su jama’a murmushi, a yanzu ina so in yi amfani da sarautar Sarauniyar Gashaka da aka nada ni don in rika taimakon mutane, musamman ma wadanda ba za su iya biyan kudin makaranta ba.
Darussan da sarauta ta koya mini
Na fahimci darussa da yawa a dangane da sarauta, na farko akwai abubuwa da yawa da ba za ka rika yi ba, saboda sarauta, saboda kuma nauyi ya hau kanka, sannan ka zama uwar al’umma damuwarsu ta zama taka, ka zama juji kowa kai zai nema.