Sarauniya Elizabeth ce ta fi dadewa a kan Sarautar Birtaniya
A shekaranjiya Labara ne jama’a a yankin Scotland suka yi wa Sarauniya Elizabeth ta Biyu tafi da shewa a ranar da ta zama Basarakiyar da ta fi dadewa a kan gadon Sarautar Birtaniya, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.Sarauniyar ta wuce kakar-kakarta, Sarauniya bictoria, wadda ta yi shekaru 63 da wata bakwai […]
A shekaranjiya Labara ne jama’a a yankin Scotland suka yi wa Sarauniya Elizabeth ta Biyu tafi da shewa a ranar da ta zama Basarakiyar da ta fi dadewa a kan gadon Sarautar Birtaniya, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Sarauniyar ta wuce kakar-kakarta, Sarauniya bictoria, wadda ta yi shekaru 63 da wata bakwai da kwanaki biyu a kan sarauta.
Da take bude wani sabon layin dogo a yankin Scotland, Saurauniyar ta ce ba ta taba tsammanin za ta kawo wannan lokacin ba a kan sarautar kuma ta gode wa kowa a kan sakonnin taya murna “masu sosai rai da su ka aika mata.”
A majalisar dokokin Biritaniya, Firaminista Dabid Cameron ya jagoranci jawabai a kan sarauniya Elizabeth, yana cewa ta jagoranci kasar cikin girma da arziki da martaba.
An daga gadar Tower bridge ta birnin Landan domin faretin jiragen ruwa a kan kogin Thames don girmama sarauniyar.
An haifi sarauniyar ce a ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 1926 kuma ta zama sarauniya a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 1952, bayan rasuwar mahaifinta Sarki George na Shida, lokacin tana da shekara 26 da haihuwa.