Sarauniyar Ingila ta hana surukarta sanya dangalallun tufafi

Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, ta umarci surukarta Kate Middleton ta daina sanya dangalallun tufaffi, musamman a daidai wannan lokaci da take shirin kai ziyara kasar Autiraliya, a cewar wakilin jaridar Dailymail, Katie Nicholl. Kuma mujallar banity Fair ta ruwaito cewa Sarauniyar ta umarci jami’ar kwalliyarta, Angela Kelly, ta taimaka wa Kate Middleton, wajen sanya abin […]

Sarauniyar Ingila ta hana surukarta sanya dangalallun tufafi

Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, ta umarci surukarta Kate Middleton ta daina sanya dangalallun tufaffi, musamman a daidai wannan lokaci da take shirin kai ziyara kasar Autiraliya, a cewar wakilin jaridar Dailymail, Katie Nicholl. Kuma mujallar banity Fair ta ruwaito cewa Sarauniyar ta umarci jami’ar kwalliyarta, Angela Kelly, ta taimaka wa Kate Middleton, wajen sanya abin wuya mai kawalniya da kayan ado irin na sarauta.
Sarauniya dai mace mai sha’awar sanya dogayen tufafi, don haka take bukatar ganin Gimbiya ta sanya tufafi da abin wuya da zai nuna martabar sarauta.
Wata majiya daga Fadar Buckingham, ta tabbatar da cewa abin wuya na lu’u-lu’u mai furen zoborodo, wani tambari ne da ke nuni da kasar Austiraliya, kuma kyauta da Sarauniya ta karbo daga kasar.