Sarauniyar Ingila ta karrama Likitan da ya yi hidimar haihuwar Yarima George
Likitan kula da lafiyar masu juna biyu da ya yi aiki, wajen haihuwar jaririn Yarima William da Gimbiya Kate, ya samu karramawa daga Sarauniyar Ingila, inda ta karrama shi tare da wata fitacciyar jarumar film, Angela Lansbury.Tunda aka fara bayar wannan lambar karramawa ta Dame a shekarar 1917, mata ke da kaso 51 cikin 100 […]
Likitan kula da lafiyar masu juna biyu da ya yi aiki, wajen haihuwar jaririn Yarima William da Gimbiya Kate, ya samu karramawa daga Sarauniyar Ingila, inda ta karrama shi tare da wata fitacciyar jarumar film, Angela Lansbury.
Tunda aka fara bayar wannan lambar karramawa ta Dame a shekarar 1917, mata ke da kaso 51 cikin 100 na wasdanda aka karrama, sai daga bisani aka fahimci babu sunayen gwarazan ‘’yan wasannin motasa jiki, wdanda suka hada da Andy Murray da Dabid Beckham.
Likitan masu juna biyu Marcus Stchell, dan shekara 70, ya dakatar da ajiye aikinsa, har sai da ya samu bayar da gudunmuwarsa wajen haihuwar Yarima George a watan Yulin bara, don haka Sarauniya ta bayar da umarnin a rika yi masa lakabin “Sir” bayan da ta karrama shi da lambar KCRb (Knight Commander of the Royal bictorian Order), wata karramawa ce ta musamman daga Sarauniya Elizabeth II.
Ita kuwa Lansbury, ‘’yar shekara 88, ita ce tsohuwar jarumar fim haifaffiyar Birtaniya da ke fitowa a matsayin Jessica Flecther a gidan talabijin din Amurka, a wasan kwaikwayon talabijin na kisan kai “Murder,” ta samu babbar karramawa da ta Dame daga daular Masarautar Birtaniya.
Sauran wadanda aka karrama sun hada da Opera Katherine, wata mawakiya da ta tara kudin tallafawa wajen kula da lafiyar tsofaffin sojoji. Sai tsohuwar ’yar fim Penelope Keith da ta yi suna a shekarun 1970, a fim dinta na kyakkyawar rayuwa, wato “The Good Life.” daukacin wadannan mutane an ba su OBE (Order of the British Empire).Mafi yawan mutum 1,195 da ke cikin jerin wadanda aka karrama ba fitattun mutane ba. Kodayake akwai Madelein Josephine Hennel da Henriette da suka yi hidima ga Firayiministocin Birniya biyar, duk an karramar masu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.