Sarauniyar Kyau: Har yanzu ji nake kamar a mafarki —Shatu Garko
Matashiyar da ta lashe kambun Sarauniyar Kyau ta Najeriya, wato ‘Miss Nigeria’ na bana, Shatu Garko, ta ce har yanzu ji take yi kamar a mafarki. Shatu Garko wadda ’yar asalin Jihar Kano ce, ita ce mace ta farko mai sanya lullubi da ta lashe kambun kuma ita ce Musulma ta farko kamar yadda Aminiya […]
Matashiyar da ta lashe kambun Sarauniyar Kyau ta Najeriya, wato ‘Miss Nigeria’ na bana, Shatu Garko, ta ce har yanzu ji take yi kamar a mafarki.
Shatu Garko wadda ’yar asalin Jihar Kano ce, ita ce mace ta farko mai sanya lullubi da ta lashe kambun kuma ita ce Musulma ta farko kamar yadda Aminiya ta kalato daga Wikipedia.
- Shatu Garko: Bakanuwa ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau
- An kulle sojar da bidiyon neman aurenta da dan NYSC ya karade gari
Shatu ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, “Ku ba ni dama in sanar da kaina. Sunana Shatu Garko, ni ce na lashe Kambun Sarauniyar Kyau karo na 44 a Najeriya.
“Ji nake yi kamar a mafarki. Na ji dadin yadda kuke nuna min kauna. Ina godiya ga ’yan Najeriya bisa kwarin gwiwa da kuka ba ni. Ina godiya har zuciyata.
“Ina godiya ga mahukuta da masu shirya gasar da suka ga dacewa ta kuma cancantata.”