Sarauta: Wadansu na nema, wadansu na gudun ta

Shi dai wannan al’amari na sarauta, wasu na ta kwazon neman, yayin da wasu ke gudun su.

Sarauta: Wadansu na nema, wadansu na gudun ta

An fara wallafawa 28 ga Disamba, 2014

Sarautun gargajiya, wadanda suka hada da Sarki da Magajin Gari da Waziri da Galadima da kaura da Madawaki da Wambai da Ciroma da Sa’i, Durbi da Ubandawaki sun dade, kusan daya suke da kafuwar kasar Hausa. 

Yayin da a kowane gari akwai irin rawar da suke takawa kamar a Katsina Galadima yana cikin masu nada sarki, ba zai iya zama sarki ba, yayin da a Kano Galadima zai iya zama sarki.

Kuma a Katsina da Daura, Magajin Gari ke zama sarki, duk da cewa wasu dalilai kan saba wannan ka’idar. Sannan akan nada masu jinin sarauta wasu mukamai kamar Ciroma, Sarkin Yaki, Waziri da kaura.

A wancan zamanin sarakuna suke yin huduba da jan salla da shari’a da sauransu. Yayin da a yau da su ake watanda da dukiyar Najeriya.

A shekaru ashirin da suka gabata, musamman daga shekara 2000, aka sauya komai inda kusan kowane wata ko mako sai an yi nadi a fadojin kasar nan.

A wani garin ba a samun baki ma sai ranar da aka ce za a nada wani hamshakin, sai otel ya cika, masu sayar da abinci su samu gwaggwabar riba, masu buge-buge su bugo fasta da stika da sauransu. A kashe kudin gaske wajen shiri da yin bukukuwan nadin sarauta.

Akan yi tunanin kudi kan ba mutum sarauta, yayin da sai ka iske hamshakai ba mukamai, wani lokacin ’yan gidan sarauta ne, amma ba nadi. Duk da cewa mutane da dama na bambantan ra’ayoyi akan muhimmancin neman sarauta.

Shi dai wannan al’amari na sarautu, wasu na ta kwazon neman, yayin da wasu ke gudun su.

Wasu manyan mutane da ba su da sarautun gargajiya sun hada da Janar Muhammadu Buhari da Lawal Kaita da  Aliko dangote da Umar Mutallib da dahiru Mangal da Aminu dantata da Abdussamad Rabiu da M.D Yusuf da Ambasada Magaji Muhammadu da Sanata Kabir Gaya da Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da Farfesa Jibril Aminu da Abdullahi Dikko Inde da Nuhu Ribadu, duk da kimmarsu a kasar nan, sannan wasu daga cikinsu suna da alaka da gidajen sarauta.

Yayin da wasu kan guji sarautun kamar yadda Sule Lamido ya sa a nada dansa hakimin Bamaina a madadinsa. Shi kuwa Injiniya Rabi’u Kwankawso mahaifinsa ne Majidadin Kano, hakimi Madobi.

Amma bai taba nuna sha’awar neman sarauta ba, ko yin girman kai don ya fito daga gidan sarauta.

Sau da yawa sai ka iske talakawa na kuka da sarki! Da irin wadanda yake nadawa a sunan sarautu, domin kusan ba wanda ake nadawa a bisa mizanin wani abu da ke kama da cancanta, kawai son rai ne, musamman idan ya biya sarkin wani abu!

Domin da zaka turke sarki ya fada fa’idar rawanin da yake nadawa, babu gamsashiyar amsa da zai iya bayarwa!

Hakan ke sa shugaban kasa ko gwamnoni yin tasiri kan wa zai zama sabon sarki, kuma su kan warware nadin da ba nasu bane, inda gwamnoni ke kotsawa fadar sarakuna, duk da hakan katsalandan ne ga majalisar sarakuna.

Bugu da kari su kansu sarakunan ba ruwansu da talakawan masarautar, su dai a basu kudi, kwangiloli da dan abin da ba a rasawa na Ramadan, ko ragunan layya! Shi yasa yana da wuya ka ji an nada wani dogari a bisa wata bajinta ko an kara masa daraja a bisa wani hobassa da ya yi.

Babu takamaimen aiki da wadanda sarakuna suke nada suke yi, nadi ne ko rawanin kawai don kulla wata alaka ta wani dalili.

Wani abin da manazarta da dama ke kallo shi ne da zaran ka sami wani abin duniya sai ka iske sarakuna sun koma karkashin ikonka, a haka suke kokarin mayar da kai dan majalisar ko ba ka je ba ka rika turo wani abu.

Duk da cewa da dama daga cikin wadanda aka ba wadannan sarautun ‘ya’yan talakawa ne, amma Allah ya arzutasu da abin duniya, a haka sun fita daga talauci su ma sun zama sarakuna!

Hakan ya haifar da sabbin sarautu da mukaman da ba a san su a baya ba. Daga nan sai aka rika dauko sarautun wasu garruruwan ana kawowa wasu garruruwan kamar yadda ake dauko sarautun Barno ana kawowa kasar Hausa.

Haka ‘yan Kudu suka rika ba gwamnonin Arewa, su ma na Arewar suka rika ba gwamnonin Kudu tare da ba shugaban kasa, har ya kai ga cewa a Nijeriya shugaban kasa baya iya kirga sarautunsa! Saboda kowane sarki kokari yake yi ya nada shi!

A hankali aka fara ba mata da maza a lokaci, a rana daya sai a gayyaci mace da mijinta a nadasu, wasu sarautun matan ma ba a taba ba kowa ba tun zamanin da aka yi su, watau zamanin jahiliya, sai ga su sun dawo a wannan zamanin!

A halin yanzu akwai wasu manyan mutane da ke da sarautu a Najeriya da Nijar, sannan wasu kuma sarakuna ba abin da yake gabansu sai nadin ‘ya’yansu da surukansu.

Kamar yadda wani sarki sai da ya tabbatar da ya nada ‘ya’yansa dozen, tare da mayar da wasu yaran hakimai. Wai ko da sun mutu sun kafa ‘ya’yan ke nan! Bayan duniya ba ta san gwani ba, koyaushe za ta iya sauya sa’a!

Ba za a manta da sarkin da ya taimaka wa talakawa ba, ya dauki ma’aikata ya gazawa mabukata, ya kulla da dangi, ya kawo wa masarautarsa ci gaba.

Abin da ya fi komai muhimmanci, shi ne, ko ba ka da rawani kimmarka na nan a matsayin da ka dauki kanka, idan kana ganin ka sami arziki ka yi kokarin kyautata wa mutane shi ne mafi a’ala ba neman nuna kanka ba, bayan baka, sai a kiyaye amanar da Allah ya danka wa mutum, domin mukami riko ne na wani lokaci.

Buhari Daure Muryar Talaka.
[email protected]

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja