Sarautar Kano: Dawo da Sanusi II yana hannun Abba —Kwankwaso

Kwankwaso ya yi tsokaci game da Masarautar Kano da Gwamnatin Ganduje ta raba zuwa masarautu biyar.

Sarautar Kano: Dawo da Sanusi II yana hannun Abba —Kwankwaso

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon Gwaman Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce gwamna mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ne yake da ta cewa kan batun dawo da Sarki Muhammadu Sununi II da Gwamnatin Ganduje mai barin gado ta sauke.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ya karade kafofin sada zumunta, inda ya yi tsokaci game da batun raba Masarautar Kano da Gwamnatin Ganduje ta yi zuwa masarautu biyar.

A cewarsa, ya rage na sabuwar gwamnatin ta duba abubuwan da suka shafi sarauta da ke bukatar gyara ta gyara su.

Ya ce, “a matsayinmu na manya za mu ci gaba da bayar da shawara domin ganin a yi abubuwa daidai yadda ya kamaa.

“A baya mun yi kokarin sanya baki game da batun nadawa ko tube sarki, kuma yanzu ga wata dama ta samu.

“Masu wannan damar su ne za su zauna su dubi al’amarin, su ga abin da ake bukata daga gare su; Bayan batun sarkin, hatta masarautar an raba ta gida biyar, wadannan abubuwa ne da ya kamata a duba.”

Kwankwaso ya yi wa Gwamnatin Abba mai jiran rantsuwa addu’ar samun taimakon Allah wajen sauke nauyin jama’ar Jihar Kano cikin sauki da nasara.

Jama’a dai na ganin tafiyar siyasar Kwankwasiyya da ta ci zaben gwamnan jihar Kano, na dasawa sosai da tubabben sarkin.

Wasu magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya wadda Kwankwaso ke jagoranta na riyawa a kafofin sada zumunta cewa da zarar sun hau mulki, gwamnatinsu za ta dawo da Sarki Sanusi II ta kuma rushe sabbin masarautun da Gwamnatin Ganduje ta kafa.

Akwai kuma wadanda ke gabatar da batun soke sabbin masarautun a matsayin bukatarsu ga gwamnati.

A baya-bayan nan dai Gwamna Ganduje mai barin gado ta aike wa majalisar dokokin jihar daftar dokar masarautun.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos