Sarautar Kano: Ga dama ga damuwa

Rasuwar  Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ta haifar da wagegen gibin da cike shi ya haifar da kuka da guda a lokaci guda a masarautar Kano a sakamakon rudanin da  ya taso saboda nadin wanda zai gaje shi. Da farko wadansu suka rika baza jitar-jitar cewa Sanusi Lamido Ado Bayero, babban dan mariyin […]

Sarautar Kano: Ga dama ga damuwa
Sarautar Kano: Ga dama ga damuwa

Rasuwar  Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ta haifar da wagegen gibin da cike shi ya haifar da kuka da guda a lokaci guda a masarautar Kano a sakamakon rudanin da  ya taso saboda nadin wanda zai gaje shi. Da farko wadansu suka rika baza jitar-jitar cewa Sanusi Lamido Ado Bayero, babban dan mariyin ne aka nada, amma da gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar wanda aka nada, sai aka ji cewa tsohon gwamnan babban banki Sanusi Lamido Sanusi ne.
Tun daga shekarar 1963 lokacin da gwamnatin farar hula ta jamhuriya ta daya ta nada marigayi Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano, an yi gwamnoni a Jihar Kano guda, amma babu wanda ya samu damar nada sarkin Kano, sai gwamna mai ci a halin yanzu  Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, sai dai kuma wannan damar da ya samu ta jawo wa wadansu damuwa a masarautar ta Kano. Domin kuwa nadin da  aka yi wa Sanusi Lamido Sanusi ya yi wa wadansu dadi kuma ya bata wa wadansu rai, wanda ya sanya wadansu suka rika kona tayoyi a babban titin da ya nufi fadar sarki tare da farfasa fitillun da ke haska hanyoyi. Al’amarin ya kusan kazancewa lokacin da magoyan Sarki Lamido Sanusi suka tinkari masu nuna adawa da nadin nasa, amma Allah Ya sanya aka shawo kan matsalar cikin sauri.
Wannan tunzurin  ne ya sanya  bayan sabon sarki Sanusi Lamido Sanusi ya karbi sandar girma da sauran muhimman abubuwa na sarauta, wadanda suka hada da Tagwayen masu da takalman fatar jimina da malafar Dabo da wata karamar wuka da takobi da alkyabbar marigayi Sarki Ado, domin kama aiki,  dole ya cigaba da zama a gidan gwamnatin Jihar Kano, duk da cewa a bisa al’ada kamata ya yi ya shiga fadar sarki a ranar uku da nada shi.
Sarki Lamido Sanusi ya yi amfani da wani bangare na gidan gwamnatin jihar Kano ne a matsayin majalisarsa, inda manyan ’yan majalisar sarki suka yi masa mubayi’a, tare da karbar manya baki da suka je Kano domin taya shi murna da kuma yi masa ta’aziyyar marigayi Sarki Ado.
Wakilan Aminiya da suka samu damar  shiga cikin gidan sarkin sun ga yadda ake ta kai-kawo wajen gyara wurin da sabon sarkin zai zauna ta hanyar share-share da kuma kinkintsa kayayyakin marigayin sarkin.
An ce hatta kayayyakin al’ada da aka ba sabon sarkin, a ranar Talata, don tabbatar masa da sarautarsa, wadanda suka hada tagwayen masu da malafar Dabo da wata ’yar karamar wuka da kuma wata igiya ta tsohon sarki, duka an fito da su daga fadar zuwa gidan gwamnati ne a boye.
Wani na kusa da fadar ya shaida wa Aminiya cewa, “Ya kamata a ce sarkin ya zo fadar a cikin mota da tawagar jama’a ’yan rakiya. Sai dai abin mamaki, a maimakon a ce sarkin ya zo fada tun ranar Talata tare da jama’a masu yi masa fatan alheri cikin yanayin nishadi, sai ga shi a daidai wannan lokaci fadar ta yi cikar dango da jami’an tsaro, wadanda suka hana shige da ficen abin hawa a fadar. Idan har aka hana abin hawa shiga fada, to ta yaya za a karbi sabon sarkin a nan? Ba zai yiwu sarki ya zo fada da kafa ba, domin ya saba wa al’adar masarautar.” Inji majiyarmu.
Kodayake babu wata sanarwa a hukumance  da ta bayyana dalilin da ya sanya sabon sarkin bai koma cikin fadarsa ba, kamar yadda ake zato, Aminiya ta gano cewa hakan bai rasa nasaba da dimbin jami’an tsaron da aka sanya suna gadin fadar sarkin ba. Domin ga dukkan alamu nadin Lamido Sanusi bai yi wa gwamnatin tarayya dadi ba, wadda ita ce take da iko da jami’an tsaro.
A ranar Lahadi, bayan an sanar da nadin  sabon sarkin, sai sojoji suka bayar da umarnin hana sauka da tashin jaragen da ba na fasinja ba a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, wanda hakan ya haifar da cikas ga manyan bakin da suke son zuwa Kano domin taya sabon sarki murna.
A ranar Litinin kuma aka sanya ’yan sanda suka zagaye fadar sarki tare da hana motoci shiga gidan sarkin. A al’ada dai Sarki Lamido zai bar gidan gwamnatin Kano zuwa fadarsa da ke Nasarawa ne a cikin jerin gwanon motoci, daga nan kuma sai ya wuce zuwa fadar sarki inda fadawansa za su tarbe shi.  Wata majiya a fadar sarkin ta bayyana wa Aminiya cewa har an kammala dukkan shirye-shirye domin kai sarki fadarsa, amma aka dakata saboda ganin dimbin jami’an tsaron da suka mamaye fadar sarkin.
Sai dai kuma Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano Adenerele Shinaba ya bayyana wa Aminiya cewa an kai ’yan sanda fadar ne domin tabbatar da tsaro, amma ba a hana kowa shiga fadar ba, kuma ba wani ne ya ba su umarnin yin haka ba.