Sarautar Kano: An dage sauraren karar Gwamnatin Kano
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta sanar da hakan bayan zaman kotun na ranar Litinin
Babbar Kotun Jihar Kano ta dage sauraron karar da gwamnatin jihar ta shigar na neman haramta wa Aminu Ado Bayero gabatar da kansa a matsayin sarkin Kano.
A ranar Litinin babbar kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Yuli, 2024.
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta sanar da hakan bayan zaman kotun na ranar Litinin.
Gwamantin Jihar ta shigar da kara ne tana neman kotu ta hana Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da takwarorinsa hudu na masarautun hudu a gwamantin ta rushe.
- Gwamnan Sakkwato na shirin tsige Sarkin Musulmi —MURIC
- Kano: ’Yan sanda sun kori ’yan tauri daga Fadar Sarki
Sauran masarautun da sabuwar dokar masarautun Kano ta soke su ne Bichi, Gaya, Karaye da kuma Rano.