Sarautar Kano: Muna da yakinin za a yi mana adalci — Aminu Bayero
Za mu tabbatar da umurnin kotu kan dakatar da rushe msauratun Kano a cewar ’yan sanda.
Sarki Aminu Ado Bayero ya yi kira ga jama’ar Kano da su kwantar hankali su kuma su zauna lafiya a yayin da ake ci gaba da takaddama kan sarautar jihar.
Aminu Bayero ya yi wannan kira ne yayin ganawa da shugabannin tsaro a Fadar Sarkin Kano da ke Nassarawa.
Sarkin wanda ya yaba wa shugabannin tsaro dangane a ziyarar da suka kai masa, ya kuma tabbatar da cewa nan gaba kadan gaskiya za ta yi halinta.
- Ana zaman ɗarɗar bayan an wayi gari da sarakuna biyu a Kano
- Masarautar Kano: Abba ya ba da umarnin tsare Sarki Aminu
Ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya a Jihar Kano da Nijeriya baki daya, yana mai kira ga Kanawa da su zama jakadu na zaman lafiya yayin da ake dakon sakamakon shari’ar tube rawaninsa da Gwamnatin Kano ta yi.
Ya kara da cewa, suna da yakinin wadanda ragamar shari’ar da za a soma sauraro kan takaddamar sarautar Kano ke hannunsu za su yi adalci.
Tuni dai jami’an tsaro a Kano suka sanar da karbar umarnin kotu da cewa za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faɗin Jihar Kano.
Cikin wani jawabin hadin gwiwa da jami’an tsaron suka gabatar wa manema labarai a shalkwatar ’yan sanda da ke Bompai, Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Usaini Gumel ya ce jami’an tsaron suna biyayya ne da umarnin da Kotun Tarayyar da ke Kano ta bayar.
Kotun Tarayyar dai ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun jihar biyar bayan shigar mata da ƙorafi kan hakan, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙarar.
Dangane da hakan ne CP Gumel ya ce jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadar.
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma yi kira ga mazauna birnin Kano da su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai, musamman yadda ya ce an san al’ummar jihar wajen bin doka da oda, kafin kotu ta yanke hukunci kan batun ranar 3 ga watan Yuni.
CP Usaini Gumel ya kuma gargaɗi duk wanda ya yi yunƙurin karya doka a jihar da cewa zai fuskanci fushin jami’an tsaro, yana mai cewa jami’an tsaron sun baza komarsu a faɗin birnin domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.