Sarautar Kano: Yadda ’yan siyasa ke gwara kan ’yan uwa

Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta cewa tana da hannu a rikicin masarautar da ke faruwa a Kano.

Sarautar Kano: Yadda ’yan siyasa ke gwara kan ’yan uwa

Sarkin Kano na 15 a daular Fulani, Alhaji Aminu Ado Bayero mahaifi yake ga Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II, domin ƙanin mahaifinsa ne, Alhaji Lamiɗo Sanusi ɗan Khalifa Sanusi I, Khalifa Sanusi I kakan Sanusi na II kuma wan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ne mahaifin Aminu.

Kuma hakan ne ya sa Khalifa Sanusi II ya taso a hannun marigayi Alhaji Ado Bayero, tare da ƙannen mahaifinsa Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero waɗanda daga baya aka naɗa sarakunan Kano da Bichi.

Bayanai sun ce ’yan uwan waɗanda suka taso a matsayin abokai sun shafe fiye da shekara goma suna kwana a ɗaki guda, kuma sakamakon shaƙuwar da take tsakaninsu ne kusan komai tare suke.

Wata majiya ta taɓa shaida wa Aminiya cewa a irin haka ne, wani lokaci sun je dubiya a makaranta a Kazaure, aka ɗaura auren Sanusi II da Fulani Ado Bayero ƙanwar Aminu Bayero.

Taƙaddamar sarautar Kano ta baya-bayan da ta haifar da rikicin a tsakanin ’yan uwan junan ta samo asali ne tun a shekarar 2014, lokacin da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu.

A lokacin masu zaɓen Sarki sun miƙa wa Gwamna Rabi’u Kwankwaso sunan mutum uku, ciki har da sunan babban ɗan marigayin Ado Bayero, wato Alhaji Sanusi Bayero da kuma Sanusi II sai dai a daidai lokacin da ake jiran sanarwa daga gwamnati, sai aka ji Jam’iyyar PDP ta Ƙasa tana taya Sanusi Bayero murnar zama Sarkin Kano, lamarin da aka ce ya fusata Gwamna Kwankwaso wanda a lokacin yake tsama da Shugaban Ƙasa Jonathan da jam’iyyarsa ta PDP.

Bayan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya zama Gwamna a zaɓen 2015, an riƙa samun takun-saƙa a tsakaninsa da Sarki Sanusi wanda ake zargi da ba ya ganin zarau sai ya tsinka.

Kuma sakamakon saɓanin ne ya jawo a ƙarshe gwamnatin Ganduje ta raba masarautar zuwa biyar, kuma ta ba Sarki Sanusi umarnin ya kira taron majalisar sarakunan jihar a matsayinsa na shugaba, amma ya ƙi kuma da hakan ne ta dogara wajen warware masa rawani, tare da tura shi gudun hijira a ƙauyen Loko da ke Jihar Nasarawa.

Sai dai Halifa Sanui II ya ƙalubalanci tura shi gudun hijirar a kotu wadda ta ce hakan ya tauye masa ’yanci don haka ta ba shi damar yana iya zuwa ya zauna a ko’ina a Nijeriya ciki har da ƙwaryar birnin Kano.

Manazarta suna ganin taƙaddamar sarautar ci gaban rigimar da ke tsakanin manyan ’yan siyasar jihar ne da suka ɓaɓe wato Ganduje da Kwankwaso musamman idan aka lura da yawancin tattaunawar da ake yi a shafukan sada zumunta, magoya bayan Jam’iyyar NNPP da Kwanwasiyya suna tare da Khalifa Sanusi II ne, yayin da magoya bayan Jam’iyyar APC da Ganduje suke tare da Sarki Aminu Bayero.

Wannan ya sa ake nuna wa juna yatsa a tsakanin magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Dokta Abdullahi Umar Ganduje, inda kowane ɓangare ke zargin ɗan uwansa da assasa rigimar sarautar.

A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa dokar masarautu ta jihar gyaran fuska, inda ta rushe sababbin masarautun jihar biyar da suka haɗa da Kano da Bichi da Rano da Gaya da Ƙaraye kuma ta dawo da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarauta — shekara huɗu bayan tuɓe shi da gwamnatin Dokta Abdullahi Ganduje ta yi.

Kuma take Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a kan sabuwar dokar lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Sai dai lamarin na ci gaba da jawo muhawara a tsakanin jama’a a ciki da wajen jihar musamman a kafafen sada zumunta inda mutane suke danganta gaba ɗayan lamarin da siyasa lura da cewa a lokacin Gwamna Abdullahi Ganduje makamancin hakan ya faru inda ya sauke Sarki Sanusi II daga sarauta tare da naɗa Sarki Aminu Bayero.

Sai dai a ranar Juma’ar makon jiya Babbar Kotun Tarayya da ke Kano a ƙarƙashin Mai shari’a A. T. Liman ta bayar da umarnin dakatar da rushe masarautun da hana naɗa kowane sarki a masarautun biyar, inda ta ce kowa ya tsaya a inda yake har zuwa lokacin da za ta saurari ƙarar da Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Ɗan’agundi ya shigar gabanta.

Duk da wannan umarni na kotu Gwamantin Jihar ta naɗa Sanusi II a matsayin sabon Sarki.

A ranar Asabar kuma sai aka ji labarin cewa Gwamna Abba Kabir da Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam da wasu muƙarraban gwamnati sun ɗauki Sanusi II cikin dare sun kai shi Gidan Rumfa da ke Ƙofar Kudu bayan samun rahoton cewa Sarki Aminu na hanyar shiga Kano inda yake harin shiga gidan.

Hakan ya sa Gwamnan ya ba Kwamishinan ’Yan sandan jihar umarnin ya kama ‘tsohon’ Sarkin in ya shigo jihar.

Sai dai Sarki Aminu ya shiga birnin tare da rakiyar jami’an tsaro da suka ƙunshi sojoji da ’yan sanda masu yawa, kuma sai aka ji Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya fitar da sanarwa cewa da doka zai yi aiki.

Hankalin mutane ya tashi a lokacin da aka ji labarin cewa Sarki Aminu zai bar gidan Sarki na Nasarawa zuwa Gidan Rumfa, inda Sarki Sanusi II yake, inda masu bibiyar lamarin suka ce da hakan ya faru, da an zubar da jini, wataƙila ma a rasa rayuka.

Kasancewar Sarki Aminu na tare da rakiyar jami’an tsaro masu yawa, su kuma magoya bayan Sarki Sanusi sun cika gidan, kuma Gwamna Abba Kabir na ciki.

Sarki Aminu ya ci gaba da zama a Nasarawa, inda ya kasance ana zaman fada biyu: Sarki Sanusi a Gidan Rumfa, Sarki Aminu a Gidan Nassarawa.

Ana cikin haka ne Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam ya zargi Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu da goyon bayan Sarki Aminu ta hanyar haɗa shi da jami’an tsaro zuwa Kano, zargin da Ribaɗu ya musantta tare da neman a janye, ko ya tafi kotu. Daga bisani Kwamared Abdulsalam ya janye tare da ba shi haƙuri.

Kotuna sun damalmala matsalar

Sarki Aminu ya koma Kano ne bisa dogaro da umarnin Babbar Kotun Tarayya da ta dakatar da cire shi ko naɗa sabon sarki shi da sauran sarakuna huɗu a umarnin da ta bayar ranar 23 ga Mayu, 2024.

An zargi Gwamnatin Jihar Kano da yin watsi da umarnin kotu inda ta ci gaba da naɗin, kuma jami’anta suka ce ba su samu umarnin kotun ba.

Sai a ranar Litinin ce gwamnatin ta ce ta samu umarnin kotun, bayan tun a ranar Alhamis Gwamna Abba ya sanya hannu a kan sabuwar dokar.

“Wannan umarni da ake ta magana a kai sai a yau (Litinin) da misalin ƙarfe 10:00 na safe ma’aikacin Babbar Kotun Tarayya a nan Kano ya kawo min shi,” in Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Haruna Isa Dederi, inda ya nanata cewa sai bayan sun aiwatar da abubuwan da kotun ta hana sannan suka ga umarninta a tattaunawarsa da BBC.

Kwatsam sai wata Babbar Kotun Jihar Kano a ƙarƙashin Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta bayar da umarni ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya fitar da Aminu Bayero daga Gidan Nassarawa tare da haramta masa kiran kansa Sarkin Kano a wani umarni da ta fitar ranar Litinin.

Washegari Talata kuma sai wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano a ƙarƙashin Mai shari’a S.A. Amobeda ta bayar da umarnin a fitar da Sarki Sanusi II daga Gidan Rumfa.

Kuma kotun ta ba ’yan sanda umarnin tabbatar da an karedukkan haƙƙoƙi da damarmaki na Sarkin Kano na 15 a zuriyar Fulani, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Umarnin ya ƙunshi hana Gwamna ko wakilansa ko waɗanda ake ƙara da ma’aikata ko wakilansu daga gayyata ko kamu ko barazana ko musguna wa mai ƙara har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci a kan ƙarar da ke gabanta.

Ita ma Babbar Kotun Jihar Kano, da ke Titin Miller ta hana ’yan sanda ko jami’an SSS ko sojoji da duk wasu jami’an tsaro daga fitar da Sanusi daga fada ko musguna masa.

Sarkin da masu zaɓen Sarki su huɗu da suka haɗa da Madakin Kano, Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Ban Kano, Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Mai Tuta, Bello Tuta ne suka kai ƙarar gabanta.

Farfaganda daga ’yan siyasa

Aminiya ta lura wasu magoya bayan APC suna yaɗa hotuna da faya-fayen bidiyo don nuna ana zanga-zanga da ƙone-ƙone a birnin, inda ’yan Kwankwasiyya ke cewa jihar na nan lafiya babu wata matsala.

Sai dai da Aminiya ta zagaya ta gano cewa lallai ana zanga­-zangar, amma babu hatsaniya, inda masu zanga-zangar suka riƙa zanga-zangarsu, sauran mutane kuma ke ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Matsayinmu Sojoji

A ɓangaren Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta cewa tana da hannu a rikicin masarautar da ke faruwa a Kano.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu a ranar Lahadin da rundunar ta wallafa a shafinta na X kamar yadda BBC ta ruwaito.

“Sabanin ra’ayin Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya reshen Jihar Kano kamar yadda jaridar Premium Times ta buga a ranar 26 ga Mayu 2024, sojojin Nijeriya ba su da hannu a rikicin Masarautar Kano kuma ba su da hannu wajen aiwatar da wani umarnin kotu.

“Sun ɗauki matakin ne kawai don daƙile duk wata matsala ko zagon kasa da za a iya samu a rikicin Masarautar Kano,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce, “Batun da ya fi ɗaukar hankalin sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro shi ne hana taɓarɓarewar doka da oda a jihar.

“Abin da sojoji ke yi a wannan mataki shi ne sa ido kan lamarin da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana idan lamarin ya ta’azzara da zai kawo barazana ga tsaron jihar da yankin baki ɗaya.” in ji sanarwar.

Wannan lamari ya janyo ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da na malaman jihar da sarakunan Arewa da ƙungiyar lauyoyi yin kira ga sarakunan biyu su yi hankali kada su bari jinin mutane ya zuba a dalilinsu.

Abin da lauyoyi ke cewa

Bayan samun umarni masu karo da juna daga kotuna biyu da suka damalmala matsalar, lauyoyi da masana shari’a sun ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

Barista Dalhatu Shehu Usman lauya ne mai zaman kansa a Kano ya shaida wa Aminiya cewa samun umarnin kotu biyu a lokaci guda abu ne na cin zarafi ga harkar shari’a.

“Idan aka samu odoji biyu daga kotuna masu matsayi daya a lokaci guda, to wannan cin mutunci ne kai-tsaye ga harkar shari’a.

“Duk da cewa ba za mu iya fadin hakan kai-tsaye ba lura da cewa akwai abubuwan da ake dubawa kafin a ce an yi wa kotu cin mutunci.

“Na farko sai idan abin da ake ƙara a kai ya zama ɗaya da waɗanda ake ƙara sun zama daya kuma za a duba a ga cewa kotunan da aka kai ƙarar dukkansu suna da hurumi. Idan waɗannan sharuɗa suka cika to an ci mutuncin kotu.”

“A wannan rigimar kotun da ta bayar da odar farko ba ta da hurumi saboda harkar sarauta harka ce da ta shafi Kano kai-tsaye.

“Amma wasu masana na ganin kotun tana da hurumi la’akari da mutanen da aka yi karar da suka haɗa da Sufeto Janar na ’Yan sanda da Shugaban Hukumar DSS da sauransu, amma a ra’ayina kotun ba ta da hurumi.

“Magana ake yi ta Dokar Masarautun Kano don haka kotun jiha ce ke da hurumi domin duk abin da mutum yake nema wannan kotun ce za ta yi masa tun daga kan nema masa ’yancinsa na ɗan Adam da sauransu.”

Ya ce, duk da cewa kotun farko ba ta da hurumi, ya kamata a yi mata biyayya, “Tunda ta riga ta ba da oda ta bayu, sai idan ita kotun ce ta janye odar ko kuma kai ka je kotun sama ka kalubalanci odar idan an yi nasara kotun ta janye ta.”

Barista Dalhatu ya kara da cewa idan aka samu oda biyu daga kotuna daban-daban to za a yi amfani da odar kotun da ta fara bayar da oda ce a kan ta biyun.

Ya ce, “Abin da ya kamata su yi shi ne su ɗauki wannan odar ta biyu su kai gaban kotun da ta bayar su nemi ta soke ta da kanta tunda dai akwai wata odar a kasa wacce ta rigaye ta. Tunda ita wannan kotu ba a gaba take da ta farkon ba.”

A cewarsa duk wanda ya shigar da qara bayan yana sane da wancan oda ta farko shi ma ya ci mutuncin shari’a.

A cewar Barsita Dalhatu Usman su ma kansu alƙalan da suke bayar da oda suna da nasu laifin.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania