‘Sardauna uba ne da kowane da zai yi alfahari da shi’

Hajiya A’ishatu Ahmadu Bello tana daya daga cikin ’ya’yan marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Aminiya ta tattauna da ita, inda ta yi bayani game da rayuwar marigayin da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Kwanakin baya ne kika cika shekara 70 da haihuwa, amma ga shi har yanzu da sauran karfinki. Wadanne […]

‘Sardauna uba ne da kowane da zai yi alfahari da shi’

Hajiya A’ishatu Ahmadu Bello tana daya daga cikin ’ya’yan marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Aminiya ta tattauna da ita, inda ta yi bayani game da rayuwar marigayin da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Kwanakin baya ne kika cika shekara 70 da haihuwa, amma ga shi har yanzu da sauran karfinki. Wadanne irin aikace-aikace kike gudanarwa a kowace rana?
Hajiya A’isha: Idan na tashi da safe  bayan na yi sallah. Ina fara gyare-gyaren gida da ayyukan da suka shafi girke-girke. Amma ba na zuwa kasuwa ko kuma tukin mota da kaina. Ni matar aure ce, kodayake, maigidana ya rasu a shekarar 1983.
Aminiya: Bayan rasuwar mahaifinku ya ya rayuwa ta kasance muku?
Hajiya A’isha: Alhamdulillah, muna rayuwa ’yan uwa da masoya suna taimaka mana.
Aminiya:  Kina da misalin shekara nawa mahaifinku ya rasu kuma ta ya ya hakan ya shafi rayuwarku?
Hajiya A’isha:  Ina da kimanin shekara 20 ne a duniya lokacin. Kodayake, kafin rasuwarsa a duk lokacin da karfe 10 na dare ya yi kuma idan ina Kaduna, mukan zauna da shi don mu tattauna. Muna tattauna al’amura da dama. Har ila yau, muna yin hakan ne tare da wasu yara saboda shi mutum ne mai kaunar yara.
Akwai wata rana na kai masa ziyara a Kaduna, sai na tsinkayi motoci da yawa a kofar gidansa. Na saba duk lokacin da na isa gidan, Sarkin Gida ko kuma Sallama zai je ya sanar da shi. Sai dai a wannan ranar bai yi hakan ba. Hakazalika, a washegari da kuma rana ta uku bayan zuwana gidan. Na kwana da sanin cewa akwai wani da yake da alhakin sanar da isowar bako. Sai na bincika ko an sanar da mahaifinmu isowata, amma sai na fahimci cewa ba a yi hakan ba. A lokacin da na tambayi dalilin rashin yin hakan. Sai Sallama cikin zaulaya ya ce abin da ya sa shi ne ai ni da shi ba ma dasawa kamar yadda yake dasawa da ’yar uwata.
Daga nan sai ya shiga ya sanar da mahaifinmu abin da ya faru. Da mahaifinmu ya ji sai ya aika aka yi kirana. Na ba shi labarin abin da ya faru. Sai wani bako da yake tare da mahaifinmu a lokacin ya ce za a ba ni wata kyauta wadda ba za a bai wa ’yar uwata wacce take dasawa da Sallama ba. Daga nan sai kowa ya fashe da dariya. A gaskiya wannan ita ce maganata ta karshe da mahaifinmu, wadda kuma ba zan taba mantawa ba.
Aminiya: Yaya kike ji a matsayinki na diyar marigayin musamman saboda kyawawan ayyukansa da ake tuna shi da su?
Hajiya A’isha: Ina jin dadi saboda irin rayuwar da yi yi lokacin da yake duniya, mutum ne da wadanda suka sansa da kuma wadanda ma ba su sansa ba duka suna kaunarsa.
Aminiya: Shin ko akwai wasu aminansa da suke raye?
Hajiya A’isha: Galibinsu sun rasu. Misali akwai Sarkin Daura Muhammadu Bashir. Kodayake, akwai wadanda suke raye kamar Galadiman Katsina Mai Shari’a Mamman Nasir. Kuma suna taimaka mana bayan ba shi. Sun dauke mu kamar ’ya’yansu, mu kuma mun dauke su tamkar iyayenmu. A kowane lokaci muke tare da su, ji nake kamar ina tare da mahaifina.
A duk lokacin da muke tattaunawa da su mukan tuna da marigayin, musamman ma Galadiman Katsina. Babu lokacin da zan ziyarce shi ba tare da ya dauko zance mahaifinmu ba.
Aminiya: Wadanne abu kika fi tuna mahaifinku da su?
Hajiya A’isha: Na fi tuna shi lokacin bikin Sallah yayin da yake kawo ziyara gida Sakkwato. Nakan tuna abubuwan da muke yi tare.  Hakazalika, ina tuna kyawawan halayensa. Muna fita tare kuma idan ina son wani abu. Idan yana da lokaci, yakan dauke ni mu je ya saya mini. Idan kuma ba shi da lokaci, yakan umarci wani da ya yi hakan. Shi mahaifi ne da kowane da zai yi alfahari da shi.
Aminiya: Idan da a ce Sardauna yana raye, wane mataki kike ganin Najeriya za ta kai a yanzu?
Hajiya A’isha: Idan da a ce sun iya  cimma irin burin da suka sanya a gaba, da a yanzu kasar nan ta kai ga gaci. Akwai ayyukan da ya fara wadanda suka gaje shi suka ki dorawa daga wurin da ya tsaya. Misali kamfanin jaridun New Nigerian da wasu kamfanoni da dama da suka durkushe.
Aminiya: Kina da shekara nawa aka yi miki aure?
Hajiya A’isha: A lokacin da aka yi mini aure na kai kimanin shekara goma sha wani abu, inda na auri Marafan Sakkwato Alhaji Muhammadu danbaba.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Hajiya A’isha: Ina da ’ya’ya biyar, kodayake, uku sun rasu. Hakazalika, ina da jikoki akalla goma sha wani abu.