Sardaunan matasan Jihar Sakkwato ya ziyarci Sarkin Samarin Yamma a Badun
Sabon Sardaunan Matasa na Jihar Sakkwato, Alhaji Mujitaba Isa Helele, wanda fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta tabbatar da nadin nasa a farkon wannan wata, ya ce zai yi amfani da matsayinsa wajen bullo da sabon salon inganta rayuwar matasa, musamman wajen rungumar ilmin addini da na zamani da zai kai su ga dogaro da […]

Sabon Sardaunan Matasa na Jihar Sakkwato, Alhaji Mujitaba Isa Helele, wanda fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta tabbatar da nadin nasa a farkon wannan wata, ya ce zai yi amfani da matsayinsa wajen bullo da sabon salon inganta rayuwar matasa, musamman wajen rungumar ilmin addini da na zamani da zai kai su ga dogaro da kai.
Sardaunan yana fadin haka ne a yayin da ya ziyarci ofishin Sarkin Samarin Yamma, Alhaji Nasiru Muhammed Yaro da ke unguwar Sabo Ibadan, domin musayar ra’ayi.
Ya ce, ziyarar ta ba shi damar fahimtar muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar matasa a jihohin Yamma. “Mun tattauna tare da musayar ra’ayi da nema da ba da shawarwari dangane da matakan wayar da kan matasan jihohinmu don ci gabansu, musamman saboda ganin matasan jihohin Kudu sun tsere mana ta fannonin ci gaba da ingattaciyar rayuwa”. Inji shi.
Alhaji Mujitaba ya ce za su bayar da tallafi ga matasa wajen neman ilmi, saboda haka ya yi kira ga matasa a Jihar Sakkwato da ma na kasa baki daya su dawo daga rakiyar zama ’yan bangar siyasa kan bukatun da ba za su amfani kasa ba. Ya kuma bukaci su koyi sana’o’i daban-daban domin dogaro da kai, wadanda su ma akwai irin gudunmawa da shawarwarin da majalisarsa ta yi alkawarin bayarwa domin cimma burin ingantacciyar rayuwar matasa.
Dangane da hukuma, Sardaunan ya nemi gwamnatocin jihohi su sake lale kan irin rikon sakainar kashin da suke yi wa matasan Najeriya. “Ya kamata gwamnatocin tarayya da jihohi su zage damtse wajen kyautata rayuwar matasa, wadanda su ne manyan gobe, kada a kyale su cikin gurbatacciyar rayuwa.” Inji shi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sarkin Samarin Yamma, Alhaji Nasiru Muhammed Yaro ya yi na’am da ziyarar Sardaunan, musamman saboda za ta kara dankon zumunci da kuma samar da mafita ga matasa wajen dogaro da kansu, kuma ya ce, “Da yawa daga cikin matasa, musamman ’yan Arewa, sun samu kansu cikin halin kunci da damuwa da talauci saboda raina sana’o’i da watsi da karatu da kananan kasuwanci suka koma ga bin yarima a sha kida. Muna amfani da wannan dama wajen yin kira ga Sarakuna Hausawa a jihohin Yamma su shawo kan matsalolin da ke tsakaninsu, su hada kawunansu don a samu cimma burin irin fafutukar da muke yi don ci gaban matasa.”