Sarki Aminu Bayero ya kai ziyara kabarin mahaifinsa

Sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara kabarin mahaifinsa  marigayi Alhaji Ado Bayero da ke gidan Sarki na Nasarawa don yin addu’a gare shi. Sarki Aminu Ado cikin rakiyar wasu daga cikin hakimansa da suka hada da Turakin Kano da Talban Kano da Dan Darman Kano, ya isa kabarin mahaifin nasa da […]

Sarki Aminu Bayero ya kai ziyara kabarin mahaifinsa

Aminu Ado Bayero

Sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara kabarin mahaifinsa  marigayi Alhaji Ado Bayero da ke gidan Sarki na Nasarawa don yin addu’a gare shi.

Sarki Aminu Ado cikin rakiyar wasu daga cikin hakimansa da suka hada da Turakin Kano da Talban Kano da Dan Darman Kano, ya isa kabarin mahaifin nasa da misalin karfe 12 :00 na ranar Talata.

Sarkin ya je ziyarar ne a wani mataki na neman tubarraki ga sabuwar sarautar da ya samu.

Sarki Aminu Ado tare da Hakimansa sun gudanar da addu’o’i ga mahaifin nasa wato marigayi Ado Bayero.

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, tare da Hakimai