Sarki Aminu ya fita wajen Kano karon farko bayan dambarwar masarauta
A halin yanzu, babu Sarki a Kano la’akari da cewa shi kansa Sarki Sanusi II ya tafi Ingila.
A karon farko tun bayan dambarwar masarauta, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya fita wajen jihar.
Bayanai sun ce Aminu Ado wanda a watan Mayun da ya gabata Gwamnatin Kano ta sauke shi daga karaga, a yanzu ya fita wajen jihar inda ya ziyarci Abuja, babban birnin tarayya.
- Bai wa ƙananan hukumomi ’yanci tamkar an bar baya da ƙura ce — Ngordi
- Ɗaliban kiwon lafiya da aka sace a Benuwe sun kuɓuta — ’Yan sanda
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa Sarkin ya fita wata ziyarar aiki ne zuwa Abuja domin halartar wani babban taro da aka gayyaci sarakuna.
Ana iya tuna cewa, Aminu Bayero ya koma Birnin Dabo kwanaki kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga karagar mulki, kuma tun daga wannan lokaci zuwa yanzu yana ci gaba da ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano.
Hakan ce ta sanya Aminu Ado ya ci gaba da zama a Fadar Nasarawa yayin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ke zama a Fadar Ƙofar Kudu ta Gidan Rumfa bayan da shi kuma gwamnatin jihar ta mayar da shi karagar mulki.
Sai dai tun bayan wannan lokaci, Sarki Aminu bai fita daga fadar ba, sai wata guda daya da ya yi a ranar 20 ga watan Yuli, inda ya halarci taron addu’o’i da saukar Alƙur’ani da aka gudanar a Masallacin Marigayi Sheikh Isyaku Rabi’u.
Tuni aka hangi Aminu Ado Bayero a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja tare da Oni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, da sauransu.
A halin yanzu, babu Sarki a kwaryar birnin Kano la’akari da cewa shi kansa Sarki Sanusi II yana birnin Ingila domin karbo shaidar karatun digirin digirgir da ya kammala a bayan nan.