Sarki Bamalli ya naɗa ɗansa sabon Walin Zazzau
Sarautar Wali a Masarautar Zazzau ita ce ta uku a cikin manyan hakimai bayan sarautar Madaki da Magajin Gari.
Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya amince da naɗin ɗansa na fari, Abdullahi Ahmed Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau.
Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Injiniya Aminu Umar wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya.
- Rashin Tsaro: Nijeriya na kunyata duniya — T.Y Danjuma
- Ƙiyayyar da ake yi wa ’yan sanda na shafar harkar tsaro a Nijeriya — PCRC
Aminiya ta gano cewa sarautar Wali a Masarautar Zazzau ita ce ta uku a cikin manyan hakimai da sarakunan masarautar ke riƙe da su bayan sarautar Madaki da Magajin Gari.
A wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Ƙwarbai, jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na masarautar ya fitar, ya ce wannan sarauta ta Abdullahi Bamalli, kakan Baban marigayi Halliru ya taɓa sarautar Walin Zazzau.
Sanarwar ta ƙara da cewa Sarkin ya kuma amince da naɗin Injiniya Sani Galadima Umar, ƙanin marigayi Walin Zazzau, Injiniya Aminu Umar a matsayin sabon Yariman Zazzau.
Idan an tuna tsohon Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru shi ne tsohon Yariman Zazzau wanda tun daga lokacin da sarki ya ɗaga darajarsa zuwa Madaki Zazzau.
Ɗan Sarki na farko kuma wanda aka naɗa Walin Zazzau, Abdullahi Bamalli, ya karanci injiniyanci ne a ɓangaren manhajar komfuta wata Software a Jami’ar Coventry da ke Birtaniya kuma yana da ƙwarewarsa a matsayin Injiniyan sadarwa a kamfanoni kamar Etisalat kuma jami’in Fasahar sadarwa a Babban Bankin Najeriya, inda ya kwashe sama da shekara 13 yana aiki
“Duk da kyakykyawan tarihinsa, Abdullahi Ahmed Bamalli ya ci gaba da mayar da hankali wajen yi wa al’ummarsa hidima, don haka matsayinsa na Walin Zazzau ya nuna cewa ya jajirce wajen ganin an tabbatar da gina al’ada, da inganta haɗin kai, da samar da haɗin kai da ci gaba a Masarautar Zazzau.”
Abdullahi wanda yake riƙe da sarautar Walin Zazzau yana da aure da ɗa.
“Za a bayyana ranar da za a naɗa rawanin Sabon Wali da Yariman Zazzau nan gaba.” Kamar yadda sanarwar ta fitar.