Sarki mara godiya

Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan ana nan lafiya. A yau na kawo muku labarin “Sarki mara godiya.” Labarin ya yi nuni ne kan yadda rashin godiya ke zame wa mutum matsala. A sha karatu lafiya . An yi wani Sarki mai tarin dukiya amma matsalarsa ita ce ba ya da godiya game […]

Sarki mara godiya

Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan ana nan lafiya. A yau na kawo muku labarin “Sarki mara godiya.” Labarin ya yi nuni ne kan yadda rashin godiya ke zame wa mutum matsala. A sha karatu lafiya .

An yi wani Sarki mai tarin dukiya amma matsalarsa ita ce ba ya da godiya game da irin dimbin dukiyar da ya mallaka.

Ran nan sai wani matsafi ya kai ziyara gidansa a cikin dare sannan ya ce da shi, shi matafiyi ne yana neman a taimaka masa da wajen kwana. Sarkin ya sanya aka ba shi wajen kwana.

Washegari sai matsafin ya ce da Sarki ko yana da wata bukata da zai biya masa domin shi matsafi ne.

Jin haka  Sarki ya ce yana son duk abin da ya taba ya zama Zinari. Sai matsafi ya ce daga lokacin komai Sarki ya taba zai zama Zinari.

Bayan matsafi ya tafi Sarki ya shiga taba komai hatta gidan nasa sai da ya koma na Zinari.

Da ma Sarki yana da wata ’ya daya kuma yana matukar son ta. Ganin yadda komai ya taba yana zama Zinari a cikin farin ciki sai ya rungumi ’yar tasa. Nan take ta koma gunkin Zinari.

Sai hankalin Sarki ya tashi nan da nan ya sa aka nemo masa matsafi. Matsafin ya ce ’yarsa za ta iya komawa yadda take amma da sharadin duk abubuwan da ya taba suka zama Zinari a baya, za su koma kamar yadda suke a da.

Nan take Sarki ya amince.  ’Yarsa da duk abubuwan da suka zama zinari suka koma kamar yadda suke a da.

Da fatan Manyan gobe za su dauki darasi daga wannan labari. Ku zama masu godiya ga Allah a duk halin da kuka tsinci kanku.