Sarki Muhammadu Sanusi II: Muhimman nasarorinsa 10 a shekara biyu
A makon jiya ne Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya cika shekara biyu a gadon sarauta. Ganin haka ne GIZAGO (08065576011) ya waiwayi baya, inda ya tattaro muhimman nasarori guda 10 da Sarkin ya samu a lokacin: Allah mai yadda Ya so, a lokacin da Ya so kuma ga wanda Ya so!Yau shekaru […]
A makon jiya ne Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya cika shekara biyu a gadon sarauta. Ganin haka ne GIZAGO (08065576011) ya waiwayi baya, inda ya tattaro muhimman nasarori guda 10 da Sarkin ya samu a lokacin:
Allah mai yadda Ya so, a lokacin da Ya so kuma ga wanda Ya so!
Yau shekaru biyu ke nan cur, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na bisa karagar sarautar kasar Kano, bayan da ya gaji marigayi Sarkin Kano, Alhaji (Dokta) Ado Bayero, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 6 ga Yuni, 2014. Bayan rasuwar tasa, abin da Allah Ya kaddara kan sarki na gaba ya tabbata, inda da maraicen ranar Lahadi, 8 ga Yuni, 2014, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ta lokacin, Rabi’u Zakariyya ya ba da sanarwar zaben sabon Sarki, Muhammadu Sanusi II.
Ba zan mance ba, a ranar Asabar, 7 ga Yuni, 2014, na shiga turakata ta Facebook, na rubuta cewa: “Ya Allah, Ka zaba mana ingantacce, nagartacce, wadatacce, gaskiyantacce, adaltacce, sahihantacce, imanantacce, tabbatacce, tausayantacce, basirantacce, karantacce a matsayin SABON SARKIN KANO. Allah Ya jikan ADO BAYERO!!!”
Ke nan SLS shi ne mai wadannan siffofi:
INGANTACCE: Domin kuwa ingancinsa ba a boye yake ba a duk duniya.
NAGARTACCE: Domin kuwa duniya ta shaida haka a tarihinsa tun daga yarintarsa har zuwa yau din nan.
WADATACCE: Domin kuwa ya wadata da kowane irin arziki, ilimi, iyali, dukiya, jama’a da sauransu.
GASKIYANTACCE: Mutum ne shi mai gaskiya, dalili ke nan ma azzalumar Gwamnatin Najeriya ta yau, ta sauke shi daga mukaminsa na Gwamnan CBN.
ADALTACCE: Mutum ne mai adalci, domin kuwa ma’aikatan da suka yi aiki da shi sun shaida haka.
SAHIHANTACCE: Mutum ne shi sahihi, mai sanin ya kamata.
IMANANTACCE: Muna kyautata masa zaton cewa shi mai imani ne da Allah da addininSa.
TABBATACCE: Domin kuwa ga shi yau Allah Ya tabbatar da shi ya zama Sarkin Kano.
TAUSAYANTACCE: Domin kuwa a bayyane take yadda ya kasance mai fito da tsare-tsaren tausaya wa talakawa da marasa galihu, a lokacin da ya rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya.
BASIRANTACCE: Domin kuwa mutum ne shi mai basira, tabbas haka ne!
KARANTACCE: Domin kuwa Sarki SLS ya karantu hagu da dama. Mai ilimi ne a addinance kuma mai ilimi ne a zamanance. Babu shakka ya karantu da ilimi. Allah Ya taya riko!”
Bayan shekaru biyu da mai martaba sarki bisa karagar mulki, a yau kuwa waiwaye za mu yi, wanda masu salon magabana ke kira da adon tafiya. A wannan waiwaye, mun yi kicibis da dinbin nasarorin da wannan hamshakin sarki ya samu a wannan zango na shekaru biyu, amma domin takaitawa, mun zabi mafiya muhimmanci guda goma. Cikin goman nan, sauran nasarorin da aka samu, wadanda ba su kidayuwa duk sun sargafu ne a kansu.
Tun farkon hawansa sarauta, nasara ta farko da ya samu, ita ce ta sake wa majalisar masarautar fasali, domin a samu sauki da dadin gudanarwa. A majalisar, ya samar da tsare-tsare masu inganci da suka danganci bangaren gudanarwa, bangaren tafiyar da al’amuran kudi da kididdiga da bangaren tantancewa da bangaren ayyuka da sauransu. Wannan muhimmin aiki da Sarki ya gudanar, ya samar da tsafta da tsari mai kyau na gudanar da al’amuran masarautar, maimakon a baya da tsarin yake haka nan sasakai.
Babbar nasara ta biyu da sarki ya samu, ita ce ta gyara albashin ma’aikatan masarautar Kano. Kafin kasancewarsa sarki, akwai ma’aikatan da ke karbar albashin da bai wuce Naira dubu hudu ba a wata. Amma saboda tausayinsa da sanin darajar na kasa da shi, ya gyara albashin, inda ya dace da Naira dubu 18 mafi karanci.
Nasara ta uku da Sarki Muhammadu Sanusi II ya samu a cikin shekara biyu na mulkinsa, ita ce yadda ya kara bunkasa dangantaka tsakanin masarautar Kano da sauran masarauntu na fadin kasar nan da wajenta. A cikin wadannan shekaru biyu, sarki ya shimfida tabarmar zumunci tsakaninsa da sauran manyan sarakuna masu daraja ta daya, inda ya rika kai masu ziyarar zumunci a masarautunsu.
Ba sai an kai ruwa rana ba, wannan ziyara ta kara dankon aminci da zumunci tsakanin su kansu sarakunan, kamar kuma yadda ta kara bunkasa martabar masarautar Kano. A sakamakon wannan ziyara, sarakuna sun kara samun martaba a idanun al’umma, kuma sun kara samun damar tattaunawa da daukar matsaya mai kyau a duk lokacin da bukatar haka ta taso, musamman ma, game da al’amuran da suka shafi al’ummarsu.
Kasancewar Sarki Muhammadu Sanusi II na kwararre ta fannin tattalin arziki, ya samu nasara ta hudu a mulkinsa na shekara biyu, inda ya kara daga martabar Kano a duniya, ta bangaren kasuwanci da tattalin arziki. Kasancewarsa mai kima a duk duniya ta fannin abin da ya shafi ilimin tsimi da tanadi, wannan ta sanya Kano ta kara fice da shahara. Balle dama Kano giwa ce a fannin kasuwanci a Najeriya da Afirika ta Yamma, don haka sunan sarki ya kara mata tagomashi a duniya.
Nasara ta biyar mai girma da sarki ya samu cikin wadannan shekaru na mulkinsa, ita ce fagen jaruntaka da saka karsashi ga shugabanni da mabiya, domin tunkarar duk wani abu da zai kawo wa al’umma barazana. karamin misali, shi ne yadda Sarki Muhammadu Sanusi II ya nuna cewa lallai ne a yaki Boko Haram, kuma lallai ne al’umma su tashi su kare kansu daga ta’addanci da ’yan ta’adda. Samun wannan kwarin gwiwa daga sarki, ya taimaka gaya wajen saka karfi da turjiyar zuciya ga al’umma.
Wata nasara ta shida da ya samu kuma wacce ta taimaka gaya, ita ce yadda ya karfafa dangantakar gidajen saraunatr da ke masarautar Kano. Ya yi haka ne, inda ya nada ’ya’yan wasu gidajen sarauta bisa mukamai; wanda a can baya har ma an fara mantawa da su. Wannan ya yaukaka dankon zumunci da ’yan uwantaka tsakanin gidajen sarautar Kano kuma ya kawo ci gaba ta wannan fuska.
Nasara ta bakwai da sarki ya samu, ita ce ta fuskar fadakarwa, yada ilimi, wanda haka ya sanya ya fita daban da sauran sarakuna. Sarki Muhammadu Sanusi II, tun hawansa karaga, bai zauna a fada kawai ba, yakan halarci tarukan yada ilimi a fadin Najeriya da waje, yana jawabai da gabatar da kasidu na ilimi ga al’umma.
Nasara ta takwas da sarki ya samu, ita ce yadda ya bunkasa dangantaka mai karfi tsakanin Jihar Kano da manyan kamfanoni na duniya.
Nasara ta tara kuwa, ita ce yadda sarkin ya zama shugaba abin koyi ta fuskar addinin Islama. Kasancewarsa masanin ilimin addinin Musulunci, ya kasance mai nuna jagoranci yadda ya dace, musamman a lokuta daban-daban, shi ke limanci, kamar kuma yadda ya kasance mai ba da ilimin addinin a duk lokacin da bukatar haka ta taso ga al’umma.
Nasara ta goma, ita ce yadda ya kasance mai jinkai da tausayin talakawa. Da dukiyarsa, tun da ya hau mulki, a duk lokacin da bukatar bayar da tallafi ya kama ga marasa galihu, ko marasa lafiya ko ga wadanda ibtila’i ya fada mawa, sarki yana yi daidai gwargwado.
Wadannan nasarori guda goma da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu a cikin shekara biyu, babu shakka abin murna ne da farin ciki. Abin da ya rage mana shi ne, mu ci gaba da yi masa addu’a, Allah Ya kara tsawancin kwana da lafiya a gadon mulki mai fa’ida. Allah Ya taimaki sarki, Allah Ya taimaki kasarmu Najeriya da dukkan malumanmu da shugabanninmu!