Sarki Sanusi ya ziyarci unguwar da mutane suka rasu a dalilin rusau

Sarkin ya nanata kiran a zauna lafiya yana mai cewa babu wani fili ko wata dukiya da za ta yi daidai da darajar ran ɗan Adam.

Sarki Sanusi ya ziyarci unguwar da mutane suka rasu a dalilin rusau

Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

“Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan ya zama karo na ƙarshe da irin haka za ta sake aukuwa.”

Sarkin ya buƙaci mazaunan da su kai zuciya nesa su bai wa mahukunta na shari’a su yi aikin da rataya a wuyansu, yana mai cewa babu abin da rikici zai haifar face ƙarin wahala.

“A duk lokacin da tarzoma ta tashi mutanenmu ne ke kwanana ciki. Babu yadda za a yi zubar da jini ko tashin-tashina su iya warware wannan matsala. Dole ne mu haɗa kai mu kare rayuwa da dukiyar al’ummarmu.

Sarkin ya hori dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa su warware tankiya da ke tsakaninsu ta hanyar shari’a tare da gabatar wa kotu ƙwararan hujjoji

A ƙoƙarin shiga tsakani don ganin an zauna lafiya, Sarkin ya sanar da kafa wani kwamiti da zai yi ruwa da tsaki da zai haɗa da wakilan dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da ciki har da Gwamnatin Kano, mahukuntan Jami’ar Bayero da jami’an tsaro da kuma shugabannin yankin.

Sarkin ya ƙara nanata kiran a zauna lafiya yana mai cewa babu wani fili ko wata dukiya da za ta yi daidai da darajar ran ɗan Adam.

Aminiya ta ruwaito cewa tuni dai ƙura ta lafa kuma jama’a sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum bayan ƙazamin rikicin da aka yi tsakanin mahukunta da mazauna yankin.

Yadda rikicin ya auku

Aƙalla wasu mutum huɗu aka ce riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙazamin rikicin da ya hautsine tsakanin mahukunta da mazauna unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Bayanai sun ce an harbe mutanen huɗu ne yayin da suka fito tirjiya kan rusau ɗin gine-ginensu da jami’an hukumar tsara birane ta Jihar Kano KNUPDA suka aiwatar.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa galibin gidajen da rusau ɗin ya shafa tuni KNUPDA ta shafa musu alamar cewa aiki zai biyo ta kansu.

Ana dai zargin cewa gine-ginen aƙalla 40 da mahukuntan suka rushe an yi su ne a kan fulotan Jami’ar Bayero da ke Kano.

Sai dai wani mazaunin yankin da ya zanta da Aminiya, ya ce tun da jimawa Hukumar ta KNUPDA ta warware wannan matsala kuma ta jaddada musu cewa a halastaccen matsuguninsu suke domin bai shiga harabar jami’ar ba.

“Mun jima da warware wannan matsala da KNUPDA. Sun tabbatar mana cewa gine-ginenmu ba su shiga harabar jami’ar ta Bayero ba.

“Amma kwatsam sai ranar Lahadi da daddare jami’an KNUPDA suka zo suka fara rusau.

“A yayin da wasu daga cikin mazauna suka yi ƙoƙarin tirjiya ne suka harbi mutum huɗu da yanzu an yi musu jana’iza. Wannan abun takaici ne.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Manajan Darekta na KNUPDA amma lamarin ya ci tura.

Kazalika, wakilinmu da ya ziyarci ofishin KNUPDA ya tarar da shi fayau a yayin da duk manyan jami’an sun ƙauracewa zuwa aiki sakamakon fargabar abin da ka iya zuwa ya komo kamar yadda wani ƙaramin ma’aikaci ya tabbatar.

“Ana cikin wani yanayi na fargaba a ofishin nan. Shi ya sa ko wurin ajiyar motoci ya zama fayau don duk manyan ma’aikatan babu wanda ya shigo.

“Yanzu haka ƙananan ma’aikata ne kawai suke zaman dabaro a ofishin ba tare da sanin madafar da za a kama ba.

Wani babban Darektan KNUPDA da Aminiya ta tuntuɓa, ya ce ba ma’aikatansu ne suka yi rusau a unguwar ba, inda ya ba da tabbacin cewa jami’ai ne daga Ma’aikatar Ƙasa da Tsara Birane ne suka aiwatar da aikin.

Haka kuma, wani jami’i daga ma’aikatar wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce wuraren da aka yi rusau mallakin Jami’ar Bayero ne kuma nan gaba kaɗan za a fitar da sanarwa a hukumance.

Mutum uku ne suka mutu — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta bakin Kwamishinan Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ta tabbatar da cewa mutum uku ne suka mutu yayin da jami’an tsaro aƙalla 30 suka jikkata a sanadiyyar tankiyar da auku a dalilin rusau ɗin.

Kwamishinan ya bayyana cewa tun farko Jami’ar Bayero ce ta nemi gwamnatin ta shiga lamarin, wanda jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, DSS da na Sibil Difens suka yi ruwa da tsaki.

Waiya ya ce an shafe fiye da shekaru 40 ana wannan kwakwazo kan halascin mallakar fulotan tsakanin mazauna yankin da kuma jami’ar ta Bayero.

Sai dai ya ce jami’ar ta fuskanci ƙalubale a ƙoƙarin da ta riƙa yi don ganin ta karɓe haƙƙinta duk da gargaɗi da wa’adin da aka bayar na neman mazaunan su tashi.

Kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da salwantar rayukan da aka samu duk da cewa mazauna yankin sun wuce gona da iri.

Sai dai a cewar Kwamishinan, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa jami’an tsaro ’yancin kare kansu a duk lokacin da rayuwarsu ta fuskanci barazana.

Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa da cewa gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.