Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi a Kaduna
Sanusi ya dawo Najeriya daga Senegal, inda aka nada shi a matsayin Halifan Tijjaniyya kasar.
Tsohon Sarkin Kano kuma Halifan darikar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusu II, ya jagoranci Musulmi Sallar Idi ranar Alhamis a Jihar Kaduna.
Jaridar Dateline da ake wallafa wa a shafin Intanet ta ruwaito cewa, an gudanar da sallar idin ne a filin da aka rushe Otel din Durba, sakamakon aikin gine da ake ci gaba da gudanarwa a Dandalin Murtala wanda aka saba bisa al’ada.
- An ceto mutum 52 da aka yi safararsu a Kano
- Murnar Sallah: Ganduje ya ’yantar da fursunoni 123 a Kano
Sarki Sanusi ya isa Jihar Kaduna ce tun a ranar Talata daga Kasar Senegal, inda aka tabbatar da nadinsa a matsayin Halifan Tijjaniyya na Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon Sarkin Kanon ya dauki al’adar kai ziyara tare da shafe tsawon lokacin a Jihar Kaduna tun bayan sauke shi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi fiye da shekara daya da ta gabata.
Aminiya ta ruwaito cewa, a yau Alhamis ce daukacin al’ummar Musulmi suka yi bikin Idin Karamar Sallah ta bana, bayan ajiye azumin watan Ramadana da suka yi a ranar Laraba.