Sarki Sanusi ya tube Ciroman Kano

A ranar Larabar da ta gabata ce Masarautar Kano karkashin jagorancin Sarkin Kano, Muhamamdu Sanusi II ta tube rawanin Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Ciroman Kano bisa zargin kin yi wa sarkin mubaya’a. A cikin wata takardar sanarwa da masarautar ta raba ga manema labarai, mai dauke da sa hannun Galadiman Kano, Alhaji Abbas […]

Sarki Sanusi ya tube Ciroman Kano
Sarki Sanusi ya tube Ciroman Kano

A ranar Larabar da ta gabata ce Masarautar Kano karkashin jagorancin Sarkin Kano, Muhamamdu Sanusi II ta tube rawanin Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Ciroman Kano bisa zargin kin yi wa sarkin mubaya’a.

A cikin wata takardar sanarwa da masarautar ta raba ga manema labarai, mai dauke da sa hannun Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi; ta bayyana cewa yin mubaya’a ga sarki babbaan abu ne a cikin tsarin shugabanci a Musulunci da kuma al’adar masarautar Kano. Tsarin masarautar Kano ya bayyana cewa duk wani mai rike da wata sarauta, wajibi ne ya yi wa sarki biyayya, kin yin hakan kuwa yana nufin ko dai mutum ya sauka daga mukaminsa don zabin kansa ko kuma sarki ya tube masa rawani.
“Idan za a iya tunawa, tun daga lokacin da Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II ya zama sarki a ranar 8 ga watan Yunin bara, dukkanin ’yan amjalisar sarki da hakimai da masu rike da sarautun gargajiya sun yi mubaya’a ga sarkin idan ban da Ciroman Kano, wadda babbar sarauta ce a jerin sarautun masarautar Kano.” Inji Galadima.
Takardar sanarwar ta kara da cewa saboda haka ne masarautar ta maye gurbin tsohon Ciroman da kaninsa, Alhaji Nasiru Ado Bayero, wanda kafin nadin nasa shi ne Turakin Kano kuma Hakimin Nassarawa.
Idan za a iya tunawa Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero ne ya nada Alhaji Sanusi Ado Bayero wanda yake baban da a gare shi a matsayin Ciroman Kano a shekarar 2000 bayan rasuwar Ciroma na wancan lokaci, wato mahaifin sarki na yanzu Alhaji Aminu Sanusi.
Haka kuma Alhaji Sanusi Ado Bayero yana daga cikin mutanen da suka nemi sarautar sarkin Kano bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Ado bayero, sai dai sarautar ta fada hannun sarki na yanzu, Muhammadu Sanusi
II.
Tun daga wannan lokaci ne Ciroman Kano Alhaji Sanusi ya bar Kano ya koma Abuja, inda har tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi mukamin Shugaban Hukumar NPA ta kasa, mukamin da ya rike na dan wani lokaci, inda Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya cire shi a kwanan nan.
Majiyar Aminiya a fadar Kano ta rawaito cewa kafin tube Ciroman, sai da masarautar ta aike ’yan uwansa zuwa gare shi don su jawo hankalinsa game da yi wa sarki na yanzu mubaya’a, sai dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Aminiya ta lura da yadda aka kewaye fadar da jami’an tsaro baya ga motocin sintiri da ke jibge a wurin don shirin ko ta kwana.