Sarki Sanusi zai iya dawowa kan sarautarsa in – Sheikh Usman Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin manyan malaman da suka sha yi magana kan rikice-rikicen da suka yi ta faruwa a tsakanin tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce in Allah Ya ga dama zai iya dawo da tubabben Sarkin kan sarautarsa: […]
Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin manyan malaman da suka sha yi magana kan rikice-rikicen da suka yi ta faruwa a tsakanin tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce in Allah Ya ga dama zai iya dawo da tubabben Sarkin kan sarautarsa:
Me Shehi zai ce kan tube Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamnatin Jihar Kano tayi?
Duk abin da mutane suke nufi ba abin da zai zartu sai wanda Allah Yake nufi ya zartu. Ainihin shi Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya gaji kakansa cikin samun sarautar Kano kuma ya gaji kakansa a cikin fita daga sarautar. Allah shi Ya shigar da shi sarautar Allah kuma ne Ya karbi sarautar. Kafin wani lokacin in Ya ga dama sai Ya maida shi kan sarautarsa. Allah Yana da ikon yin haka, domin kakansa ya fita an kai shi Azare ya yi shekaru, daga baya da gwamnati ta canja aka je aka dauko shi daga Azare aka dawo da shi Wudil. A lokacin da gwamnati ba ta shiri da Sarkin Kano na lokacin sarautarsa za a mayar masa, amma da yake ana shiri da Sarkin Kano na lokacin Ado Bayero ba dama a ce an cire shi an maida wa Sarki Sanusin.
Me kake fata ke nan ga tsohon Sarkin?
Abin da muke fata dai Allah Ya saka da alheri amma su wadanda suka yi wannan abu ba mu ji dadin abin da suka aikata ba, saboda ba mu da iko sai abin da Allah Ya yi, amma muna da addu’a. Allah Ya kiyaye Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Allah Ya ba shi alheri. A yanzu Allah Ya kawo wani zamani wai zamanin siyasa. Ma’anar siyasar dimokuradiyya, kuma abin haushi ana bin hakkin hukuku amma ba a bin hakkin hududu. Sun ce sha’aninsu ba na addini ba ne sboda haka da hukuku da hududu duk daya ne a wurinsu. Abin da ya sa aka kafa mulkin siyasa duk duniya don kada a yi mulkin kama-karya; a ce abin da Sarki yake so shi za a yi, abin da Sarki ba ya so ba za a yi ba. Saboda haka aka yi masa majalisu, akwai ta dattawa akwai ta wakilai, duk dai don kada a yi kama-karya, amma irin abin da aka yi a Kano yana kama da kama-karyar wato ainihin siyasar ba ta yi amfani ba ke nan, saboda haka muna fata in sun samu mulki, ’yan siyasa su rika kwatatanta adalci, kada a yi kama-karya irin wanda ba a so din. Abin da muke fada musu ke nan amma duk abin da ka ga ya faru haka Allah Ya nufa. In ka samu Allah , in ka rasa Allah , in ka hau Allah , in ka rasa Allah, komai dai na Allah ne.
Me Shehi zai fada ga jama’ar Kano?
Muna kira ga jama’ar Kano kada a tada hankali kada a ce za a yi zanga-zanga ko wani abin da za a yi alhini, a yi addu’a Allah Ya yi mana mafita. Tunda abin ya faru muke ta aika wa mutanenmu a Jihar Kano a fada wa kowa kada a tada hankali. Shi kuma Sarki Muhammadu Sunusi II wannan kaddara ce Allah Ya riga Ya kawo ta, mun ga yadda ta zo ba mu san karshenta ba. Mu dai muna rokon Allah Ya kiyaye mu. Yanzu tunda babu gwamnati a hannunmu mu ne ihunka banza, abin da muka yi duk ba za a saurare mu ba. Sarki Allah Ya saka masa da alheri Allah Ya masa da alheri a duk inda Yake Allah Ya kwantar masa da hankalinsa. Allah Ya masa alheri a cikin sauran rayuwarsa, Allah Ya gyara rayuwarsa bayan wannan.