Sarki ya kare kansa dangane da zargin kashe magajinsa
Akibio na Ilora, Oba Stephen Olufemi Oyeniyi Oparinde na II, ya fasa kwai a kan zargin da wasu talakawansa suke yi cewa yana da hannu wajen kashe magajinsa, Onisa na Ilora, marigayi Cif Lawrence Owoade; wanda ya mutu watanni 15 da wucewa bayan ya rataye kansa.A watan jiya ne wasu dangin marigayin suka yi yunkurin […]
Akibio na Ilora, Oba Stephen Olufemi Oyeniyi Oparinde na II, ya fasa kwai a kan zargin da wasu talakawansa suke yi cewa yana da hannu wajen kashe magajinsa, Onisa na Ilora, marigayi Cif Lawrence Owoade; wanda ya mutu watanni 15 da wucewa bayan ya rataye kansa.
A watan jiya ne wasu dangin marigayin suka yi yunkurin tono gawar basaraken a karo na 3, domin sake yi masa jana’izar karramawa amma ba su samu nasarar yin haka ba, wanda ya janyo zargin cewa da sanin sarkin ake yin haka.
Da yake kare kansa a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a fadarsa da ke garin Ilora a Jihar Oyo, Oban ya ce tun farko ya yi gum da bakinsa dangane da wannan al’amari ne amma yanzu lokaci ya yi da zai fasa kwai. Ya ce: “Babu kanshin gaskiya a kan wannan zargi da ake yi, domin a bata mani suna. Abin bakin ciki ne da irin wadannan kalamai suke fitowa daga bakin wasu mutane da suke zargin hannuna a game da mutuwar magajina. Tabbataccen bayanin da ya ba zu a gari, wanda kowa ya sani shi ne, watanni 2 kafin Cif Lawrence Owoade ya rataye kansa, sai da ya fara kwankwadar wani abu da ake zaton guba ne. ’Yan uwansa ne suka zo suka sanar da ni batun mutuwar tasa, wanda na umarce su da su sanar da ’yan sanda. Duk da yake ba su dawo sun yi mani bayani ba amma na tabbata cewa ’yan sanda sun yi aikinsu kamar yadda ya kamata a wancan lokaci. Kamar yadda al’adarmu ta tanadar a kasar Yarbawa, ba a tsumayen Sarki ya gane wa idanunsa gawa. dan uwan marigayin da suke uba daya, Cif Layiwola Owoade daga gidan sarauta na Onisa, shi ne ya jagoranci danginsu su fiye da 40 da suka yi masa jana’iza. Bayan sun binne shi ne suka dawo har da matarsa a cikinsu suka sanar da ni cewa, sun gayyaci dodanni da suka aiwatar da irin tsubbun da ake yi wajen binne gawar mutumin da ya kashe kansa. Babu abin da na sani dangane da mutuwarsa da binne gawar.”
Dangane da zargi na biyu, cewa fadarsa ce ta ki yarda a tono gawar marigayin sai sarkin ya ce: “Daga cikin duka ’yan uwan marigayin da suke so a tone kabarin nasa, babu wanda ya taba zuwa gare ni domin neman izinin yin hakan. Idan suka sanar da ni kuma suka nemi izinin yin haka babu abun da zai hana a kyale su su yi abin da suke so.”
Jagoran zuriyar gidan sarauta na Onisa, Pa Olayiwola Owoade, ya ce: “Ba mu zargi kowa da kashe shi ba, lokacinsa ne ya zo karshe. Kuma daga cikinmu babu wanda ya kyamaci batun tono gawar tasa, sai dai wajibi ne a bi hanyoyin da suka kamata wajen yin haka.”