Sarkin Bakan Gombi ya rasu yana da shekaru 100
Marigayin ya taka muhimmiyar rawa yaƙi da ta’addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Alhaji Muhammadu Abdullahi, wanda aka fi sani da Sarkin Bakan Gombi kuma fitaccen jagoran mafarauta a Najeriya, ya rasu yana da shekaru 100.
Marigayin ya yi suna a matsayin jajirtaccen maharbi wanda ya shafe sama da rabin rayuwarsa yana fafatawa da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci, ciki har da Boko Haram, masu garkuwa da mutane da kuma ’yan fashin daji.
Rasuwarsa ta haifar da babban giɓu a fannin tsaron gargajiya, musamman a Arewa maso Gabas, inda ya yi fice wajen jagorantar yunƙurin daƙile hare-haren ’yan ta’adda.
A rayuwarsa, ya kasance Shugaban Kungiyar Mafarauta ta Kasa, inda ya jagoranci ayyukan tsaro na al’umma cikin kwarewa da hangen nesa.
An haife shi a shekarar 1926 a Ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno, kafin daga bisani ya koma Gombi a Jihar Adamawa a shekarar 1979, inda ya fara haɗa kan mafarauta domin kare yankuna daga hare-haren ’yan bindiga.
Lokacin da rikicin Boko Haram ya tsananta a shekarar 2015, Baba Gombi ya jagoranci mafarauta zuwa sahun gaba, inda suka taimaka wa sojoji da jami’an tsaro wajen ƙwato garin Gombi da wasu yankuna daga hannun ’yan ta’adda.
A ƙarkashin jagorancinsa, mafarauta sun taka muhimmiyar rawa wajen tattara bayanan sirri da kai hare-hare cikin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.
Baya ga yaƙi da ’yan ta’adda, ya kuma jagoranci ayyukan ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, inda ya kai samame cikin dazuka domin kuɓutar da su.
A shekarar 1987, marigayi Lamidon Adamawa, Alhaji Aliyu Mustapha, ya karrama shi da sarautar Sarkin Yaƙin Bindigan Arewa saboda jarumtaka.
Haka kuma, a shekarar 2018 aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Ƙungiyar Mafarauta ta Ƙasa.
An san Baba Gombi da jajircewa, tawali’u da kishin ƙasa.
Ya rasu ya bar mata huɗu, ’ya’ya 36, jikoki 56 da sauran jininsa guda 30.
Da yake jajanta rasuwarsa, Shugaban Ƙungiyar Mafarauta ta Ƙasa reshen Gombe, Rabi’u Baushe, ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi, yana mai cewa gudunmawar da ya bayar ba za ta taɓa gushewa ba.
Yayin da al’umma ke jimamin rasuwarsa, tarihinsa na ci gaba da kasancewa abin koyi ga masu ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.