Sarkin Beli ya rasu bayan shafe shekara 91 a kan mulki

Ya rasu yana da shekara 111 a duniya, bayan ya shafe shekara 91 a kan karagar mulki.

Sarkin Beli ya rasu bayan shafe shekara 91 a kan mulki

Sarkin da ya fi kowa daɗewa a kan karagar mulki a Jihar Bauchi, Alhaji Muhammadu Inuwa, ya rasu.

Inuwa, shi ne Sarkin Beli a Ƙaramar Hukumar Shira, kuma ya rasu a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, a Ƙaramar Hukumar Katagum.

Ya rasu yana da shekara 111 a duniya, bayan ya shafe shekara 91 a kan karagar mulki.

Limamin Beli, Liman Musa Abubakar, ya tabbatar da rasuwarsa, inda ya bayyana hakan a matsayin babban rashi ga al’ummar Arewacin Najeriya.

A wata hira da ya taɓa yi da Aminiya, marigayin ya bayyana tarihinsa da yadda ya hau karagar mulki.

Ya ce kakansa ne ya fara zama Sarkin Beli, inda ya yi mulki na tsawon shekara 12.

Bayan rasuwar kakansa, mahaifinsa ya gaje shi inda ya yi mulki na tsawon shekara 17.

A shekarar 1933 yana ɗan shekara 19 kacal, Sarkin Katagum, AbdulQadir, ya naɗa shi Sarkin Beli.

A lokacin mulkinsa, Inuwa ya yi aiki tare da sarakuna masu daraja ta farko har guda huɗu a masarautar Katagum.

Ya yi shekara 12 tare da Sarkin Katagum AbdulQadir, shekara 35 tare da Sarkin Umaru Faruqu.

Hakazalika, ya yi shekara 38 tare da Sarkin Muhammadu Kabiru, sannan ya yi shekara shida tare da Sarkin Katagum na yanzu, Umaru Faruq II.

A wata hira da aka yi da shi, marigayin ya ce, ya yi mulki cikin zaman lafiya tsakaninsa da al’ummarsa.

“Na shafe kusan shekara 91 a kan mulki. Alhamdulillah, muna zaune lafiya da mutane. Na haifi ’ya’ya 11; wasu sun rasu, amma bakwai suna raye – maza huɗu da mata uku.”

Jama’a sun bayyana shi a matsayin sarki mai zaman lafiya, wanda ke sauraron jama’arsa, wanda ya jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummarsa.

Sarkin Beli ya rasu bayan shafe shekara 91 a kan mulki

Rashin aiki ya ƙaru zuwa kashi 4.3 a Najeriya — NBS

Mahara sun kashe mutane 30 a hare-haren Benuwe

An ɗaure matashi shekara 8 kan satar wayar taransufoma