Sarkin Birnin Gwari ne Amirul Hajjin Jihar Kaduna na bana

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya nada Mai martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari a matsayin Amirul Hajjin Jihar na bana.Kuma Gwamnan ya amince da tura jami’an da za su tallafa wa maniyyata aikin Hajjin da za su raka maniyyatan daga jihar su 116 zuwa kasa Mai tsarki.Wannan bayani na dauke ne […]

Sarkin Birnin Gwari ne Amirul Hajjin Jihar Kaduna na bana
Sarkin Birnin Gwari ne Amirul Hajjin Jihar Kaduna na bana

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya nada Mai martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari a matsayin Amirul Hajjin Jihar na bana.
Kuma Gwamnan ya amince da tura jami’an da za su tallafa wa maniyyata aikin Hajjin da za su raka maniyyatan daga jihar su 116 zuwa kasa Mai tsarki.
Wannan bayani na dauke ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Mista Samuel Aruwan ya fitar.
A cewar sanarwar gwamnatin jihar ta yi nasarar ajiye rarar sama da Naira miliyan 200 sakamakon dakatar da daukar nauyin wasu jama’a don gudanar da aikin Hajjin bana.
Ta kara da cewa gwamnati ba ta son yin shiggi ne ga shirye-shiryen aikin Hajji da aka fara tun kafin sabuwar gwamnati ta hau ragamar mulki.
“Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril ne Amirul Hajjin shekarar 2015. Gwamnati ta kiyayi yin shisshigi da shigo da sabon tsari domin gudun daburta tsarin da aka shirya na aikin Hajjin na 2015 a jihar. A shekaru masu zuwa gwamnati za ta duba hanyoyin rage yawan kashe kudi tare da inganta jin dadin maniyyatan jihar. A bana maniyyata 5,682 ne za su sauke faralli daga jihar. Kuma jami’ai 116 gwamnati ta dauki nauyi domin kula da su a kasa Mai tsarki,” inji sanarwar.
Sanarwar ta ce gwamnati ta lura da amfanin daukar nauyin jami’an da za su taimaka wa maniyyata a nan gida da kasa Mai tsarki ne domin maniyyata su samu damar yin Hajji karbabbe.
“Wannan ya sa gwamnati ta amince ta sauke nauyin da ke kanta na tura tawaga tare da maniyyatantan zuwa kasa Mai tsarki da suka hada da malamai masu wa’azi da likitoci da ’yan jarida da mudawwafai,” inji sanarwar.
Sanarwar ta nanata kudirin kawo karshen raba kujerun Hajji da gwamnati ke yi duk shekara ga wasu mutane a jihar.
Ya ce kin raba kujeru ba shi ke nuna rashi ko kin ba da kyakkyawan kula ga maniyyatan da suka biya kudinsu domin sauke faralli daga jihar ba.