Sarkin Dass ya bukaci matasa su kasance masu rikon amana

Mai martaba Sarkin Dass da ke Jihar Bauchi Alhaji Usman Bilyaminu Othman ya bukaci matasan Najeriya su zamo masu gaskiya da rikon amana a al’amuransu na yau da kullum.Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin wankar sarautar Mataimakin Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Bauchi Malam danlami Baban Takko wanda aka ba shi […]

Sarkin Dass ya bukaci matasa su kasance masu rikon amana
Sarkin Dass ya bukaci matasa su kasance masu rikon amana

Mai martaba Sarkin Dass da ke Jihar Bauchi Alhaji Usman Bilyaminu Othman ya bukaci matasan Najeriya su zamo masu gaskiya da rikon amana a al’amuransu na yau da kullum.
Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin wankar sarautar Mataimakin Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Bauchi Malam danlami Baban Takko wanda aka ba shi Falakin Dass na farko.
Da yake amsa tambayoyin wakilinmu Sarkin na Dass ya ce ya kamata matasa su guji shan miyagun kwayoyi da tada zaune-tsaye, domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani sai da matasa masu ilimi da sanin ya kamata.
Malam danlami Baban Takko ya bayyana wa wakilinmu cewa ya yi matukar farin ciki bisa yadda Sarkin Dass ya nada shi Falakin Dass na farko kuma zai ci gaba da ba da tasa gudunmawa wajen daukaka masarautar Dass.
Malam danlami wanda fitaccen dan jarida ne da ya yi aiki a kafafen watsa labarai da dama kafin nada shi mai taimaka wa Gwamna Yuguda kan harkokin watsa labarai daga baya an nada shi Mataimakin Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya