Sarkin Dass ya nada Dokta Gital sarautar Mazawaje

Mai martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman ya nada Shugaban Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Bauchi, Dokta Ilyasu Aliyu Gital a sarautar Mazawajen Dass na farko, saboda kokarinsa na bunkasa aikin gona a jihar da kasa baki daya.A jawabinsa a wurin nadin ranar Asabar din makon jiya Alhaji Usman Bilyaminu ya yaba himmar […]

Sarkin Dass ya nada Dokta Gital sarautar Mazawaje

Mai martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman ya nada Shugaban Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Bauchi, Dokta Ilyasu Aliyu Gital a sarautar Mazawajen Dass na farko, saboda kokarinsa na bunkasa aikin gona a jihar da kasa baki daya.
A jawabinsa a wurin nadin ranar Asabar din makon jiya Alhaji Usman Bilyaminu ya yaba himmar Dokta Gital a fannin gudanar da binciken bunkasa harkar gona a kasar nan da kuma kasashen waje, lamarin da ya sa ya ga ya dace ya ba shi wannan sarauta domin kara kusanto da shi ga al’umma ya ci gaba da bayar da gudunmawa.
Ya shawarci sabon Mazawajen ya rike jama’arsa da muhimmanci tare da bayar da duk gudunmawar da ta dace a fannin ciyar da yankin gaba, musamman saboda ganin yadda yankin Dass ya shahara wajen noma.
Dokta Ilyasu Gital ya gode kan karrama shi da masarautar ta yi, kuma ya yi godiya ga manyan baki da ’yan uwa da abokan arziki da suka je domin taya shi murna.
Ya ja hankalin ’yan boko su rike noma da kiwo kada su dauka don suna cikin gwamnati za su bar neman hanyar dogaro da kai koda sun bar aiki. “Noma ce sana’a ta dindindin, hatta man fetur da ake dogaro da shi a wannan lokaci abu ne mai karewa, amma nomada aka gada tun farkon duniya haka za a ci gaba da yin ta har karshen rayuwa. Haka kuma a kullum jama’a karuwa suke yi a duniya da dole su bukaci abinci da abin sha da sutura da rayuwa da noma ke samarwa,” inji shi.
Shugaban kwamitin nadin sarautar Alhaji Waziri Yahaya Jalam ya gode wa Masarautar Dass saboda la’akari da gudunmawar sabon Mazawajen har ta nada shi kan wannan sarauta.