Sarkin Deba ya yaba wa dankwambo kan gina musu hanya da firamare ta zamani
Mai Martaba Sarkin Deba a Jihar Gombe Alhaji Abubakar Waziri Mahdi ya yaba wa Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo kan mayar da makarantar firamaren garin Deba ta zamani. Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a fadarsa a garin Deba inda ya kuma yaba wa Gwamnan kan gina hanyar […]
Mai Martaba Sarkin Deba a Jihar Gombe Alhaji Abubakar Waziri Mahdi ya yaba wa Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo kan mayar da makarantar firamaren garin Deba ta zamani. Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a fadarsa a garin Deba inda ya kuma yaba wa Gwamnan kan gina hanyar garin Deba wacce ya ce sun shafe fiye da shekara 29 suna neman a gina ta amma ba su samu ba sai yanzu. “Mu jama’ar Deba mazanmu da mata, yara da manya ba mu da wata kalma da za ta iya bayyanar godiarmu ga Gwamna dankwambo kan gina wannan makaranta da kuma hanya da muka jima muna jira,” inji Sarkin. Ya yi kira ga iyaye su kara himma wajen kai ’ya’yansu makaranta, ya ce tarihi ya nuna daga elementare ko firamare ta Gombe da ake da ita ta biyun a Deba take sai ta Dukku take biye musu, don haka su muanen Deba suna kula da ilimin zamani, ya ce yanzu haka iyaye jira suke yi a bude makaranta su kai ’ya’yansu “Don haka ina kira ga mutanenmu na kauyuka su kawo ’ya’yansu tunda an samu makaranta mai kyau don su samu ilimi mai inganci,” inji shi. Sai ya yi kira ga malaman makaranta kan su rike aikinsu da amana su karantar da ’ya’yan mutane kamar yadda iyayensu suka ba su amanarsu, ya ce su koya wa yaran da’a da ladabi da biyayya domin malamin makaranta ba ilimi kadai yake koya wa yara ba, an san shi da koya da’a da ladabi.