Sarkin Dubai ya gana da yarinyar da ke kwaikwayonsa

Sarkin Dubai Shaikh Mohammed ya gana da yarinyar da ke kwaikwayonsa tun farkon wannan shekarar, inda aka baza hoton bidiyonta. Yarinyar mai suna Muhra Ahmed Al Shehi ta samu damar maimaita abin da sarkin ya fada a gaban sarakunan kasashen Larabawa da ke fadin duniyar nan. Shi kuwa Shaikh Mohammed ya baza hoton bidiyon a […]

Sarkin Dubai ya gana da yarinyar da ke kwaikwayonsa
Sarkin Dubai ya gana da yarinyar da ke kwaikwayonsa

Sarkin Dubai Shaikh Mohammed ya gana da yarinyar da ke kwaikwayonsa tun farkon wannan shekarar, inda aka baza hoton bidiyonta. Yarinyar mai suna Muhra Ahmed Al Shehi ta samu damar maimaita abin da sarkin ya fada a gaban sarakunan kasashen Larabawa da ke fadin duniyar nan.

Shi kuwa Shaikh Mohammed ya baza hoton bidiyon a makon jiya, inda yarinyar ta rika maimaita abin da sarkin ya rika furtawa a jawabinsa, har kuma da yadda ya nuna bukatarsa ta son ganawa da ita.
“Wannan karamar yarinya ta burge ni. Allah Ya albarkace ta. Ina sha’awar kai mata ziyara, shin ko wani ya san ko ita wace ce?
Wannan al’amari na Sarkin Dubai ya yi nuni da cewa ba ya cikin shugabannin kasashe da ke yin nesa da al’ummarsu. Mai martaba Shaikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, wanda shi ne mataimakin Shugaban kasar Hadaddiyar daular Larabawa, Firayiminista, kuma Sarkin Dubai yakan yawata, ya tuka motarsa a bainar jama’a ba tare da wasu gungun jami’an tsaro da za su kange jama’a daga gare shi.

Hadimin Gwamnan Kano ya sauya sheƙa zuwa APC

Har yanzu akwai mutanen da suka maƙale bayan ambaliyar Maiduguri —Ndume

’Yan bindiga sun ƙone ofishin ’yan sanda da bam a Anambra

Tinubu ya kai ziyarar jaje Maiduguri