Sarkin Dubai ya tufatar da yara miliyan biyu da rabi a fadin duniya
Sarkin Dubai, Shaikh Mohammad Bin Rashid Al Maktoum, Mataimakin Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kuma Firayiministan kasar, ya tufatar da mutumn miliyan biyu da dubu 550, sabanin yadda ya kuduri aniyar tufatar da mutum miliyan guda a fadin duniya.Firayiministan na UAE, ya kaddamar da shirinsa na tufatar da al’umma a cikin watan Ramadana da […]
Sarkin Dubai, Shaikh Mohammad Bin Rashid Al Maktoum, Mataimakin Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kuma Firayiministan kasar, ya tufatar da mutumn miliyan biyu da dubu 550, sabanin yadda ya kuduri aniyar tufatar da mutum miliyan guda a fadin duniya.
Firayiministan na UAE, ya kaddamar da shirinsa na tufatar da al’umma a cikin watan Ramadana da ya gabata, inda ya kuduri aniyar tufatar da mabukata miliyan daya a fadin duniya. Bayan da ya tara kudi har Dirhami miliyan 122.3, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 489, ya danka alhaki tufatar da mabukatan a hannun kungiyar agaji ta Red Crescent, wadda ta yi amfani da kudin, don aiwatar da shirin.
A taron ’yan jarida da aka gabatar, Dokta Mohammad Ateek Al Falahi, Sakatare-Janar na kungiyar Red Crescen da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta “UAE,” ya bayyana yadda aka tara kudi har Dirhamimiliyan 122.3.
“A tara kudi Dirhami miliyan 122 da dubu 300, wadanda aka yi amfani das u wajen tufatar da mutum miliyan biyu da dubu 550, a kasashen duniya 51, a nahiyoyin Afirka da Asiya Turai da Kudancin Amurka,” inji shi.
Al Falahi y ace, wannan shirin, wani bangare ne na shirye-shiryen Shaikh Mohammad Bin Rashid Al Maktoum na taimakon mabukata kananan yara a fadin duniya, ta hanyar taimakawa wajen kula da lafiyarsu da ba su ilimi.
A cewarsa: “Wannan shirin manufa ce ta jawo hankalin al’umma wajen taimakon kananan yara mabukata da ke fadin duniya, musamman a irin wannan yanayi da yankin ke fama da mawuyacin hali. Maimartaba ya yi amfani da mu don kaddamar da shirinsa na bayar da agaji, musamman a lokacin watan Ramadana, don ya cusa farin ciki ga yara mabukata a wata mai alfarma.”
A kasashen Afirka 21, an tufatar da yara dubu 930 da 300, inda aka kashe kudi har Dirhami miliyan 57 da dubu 35. kasashen dai sun hada da Masar da Sudan da Mauretaniya da Djibouti da Chadi da Ghan da Sengal da sauransu.
A nahiyar Asiya, an tufatar da yara miliyan daya da dubu 530, a kasashe 19, wadanda suka hada da Iraki da Jordan da Lebanon da Falasdinu da yemen da Filifins da Maldibes da bietnam da Malesiya da Indiya da sauransu. Kuma an kashe kudi Dirhami miliyan 57 da dubu 870.
Sai kuma nahiyar Turai, inda aka talafa wa yara miliyan 49 da dubu 5559, a kasashe takwas wadanda suka hada da Romania da Albaniya da Turkiyya da Kosobo. A Kudancin Amurka kuwa, an kashe Dirrhami miliyan biyu da dubu dari 900 da 90, inda aka tufatar da yara dubu 38, a kasashen Mekziko da Brazil da Chile.