Sarkin Dutse ya hori jama’a su ji tsoron Allah
Kimanin Sarakunan Arewa shida ne suka halarci bikin cikar Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi shekara 20 a karagar mulki.Da yake jawabi a dandalin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse, Sarkin na Dutse ya ce babu abin da zai ce sai godiya ga wadanda suka je wajen taron, musamman sarakunan da […]
Kimanin Sarakunan Arewa shida ne suka halarci bikin cikar Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi shekara 20 a karagar mulki.
Da yake jawabi a dandalin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse, Sarkin na Dutse ya ce babu abin da zai ce sai godiya ga wadanda suka je wajen taron, musamman sarakunan da suka amsa gayyatarsa.
Ya kuma shawarci jama’ar masarautarsa da su ji tsoron Allah, su zama masu da’a da yi wa manya biyayya. Kuma ya bukaci su dage wajen neman ilimin addini da na zamani, domin kamar yadda ya ce, sai da ilimi ne ake yin bautar Allah.
Sarkin ya hori jama’arsa da su dage wajen inganta zumunci a tsakaninsu da ’yan uwansu. Ya kuma shawarci magidanta su mayar da hankali wajen ba iyalansu kulawa ta musamman. Kamar kuma yadda ya nemi iyaye su kula sosai wajen inganta tarbiyyar ’ya’yansu.
Shi ma a nasa jawabin, Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, cewa ya yi akwai alaka mai kyau tsakanin gwamnatin jihar da masarautar Dutse. Ya ce gwamnatinsa tana alfahari da irin gudunmawar da fadar Sarkin take ba gwamnati wajen yaki da cutar foliyo. Ya kuma hori iyayen yara su sanya yaransu a makaranta. “Sanya yara a makaranta zai taimaka wajen gyara tarbiyyarsu kuma ya samar da ilimin zai taimaka wajen hana gurbatar tarbiyyar yaran zuwa shaye-shaye da ake fama da shi a yanzu,” inji Gwamnan.
Ya bukaci Sarkin, ya ci gaba da yi wa jama’a ayyukan alheri na zakka da masarautarsa take amsa daga mawadata, take raba wa marasa galihu.