Sarkin Dutse ya nada Sarkin Bariki

Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya nada Jami’in Hulda da Jama’a na masarautarsa Malam Abba Marabusawa a matsayin Sarkin Barikin Dutse.Ita dai wannan sarauta tana da dogon tarihi, inda tun zamanin Turawan mulkin mallaka masarautar take da wannan sarauta amma aka jingine ta na tsawon lokaci sai yanzu da Mai martaba sarkin […]

Sarkin Dutse ya nada Sarkin Bariki
Sarkin Dutse ya nada Sarkin Bariki

Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya nada Jami’in Hulda da Jama’a na masarautarsa Malam Abba Marabusawa a matsayin Sarkin Barikin Dutse.
Ita dai wannan sarauta tana da dogon tarihi, inda tun zamanin Turawan mulkin mallaka masarautar take da wannan sarauta amma aka jingine ta na tsawon lokaci sai yanzu da Mai martaba sarkin ya farfado da ita.
Wadanda ba su san manufar sarautar ba, sun rika yi mata fassara ta daban, amma sarautar tana nufin Sarkin wani zango da Turawa suka zauna suka yi gidajensu wanda ake cewa wajen bariki kuma wurin wani shi ne inda fadar Mai martaba Sarkin Dutse take a yanzu.
Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya shawarci sabon Sarkin Barikin da ya rike sarautarsa da muhimmanci kuma ya zamo mai kare mutuncin masarautar tare da guje wa yin duk wani abu da zai zubar wa masarautar suna a idon jama’a.
Ya kuma hore shi ya zauna da jama’a lafiya kuma ya ci gaba da yi wa fada biyayya kamar yadda yake yi wa masarautar a baya.
Da yake jawabin godiya Sarkin Bariki Abba Marabusawa ya yi alkawarin yin aiki tukuru don kare martabar masarautar, kuma ya nemi abokai da ’yan uwa su taimaka masa da shawarwari nagari tare da yi masa addu’ar alheri don ya kai ga nasara.