Sarkin Fika ya nada Wakili na Musamman a masarautarsa

Mai martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, ya tabbatar da nadin Alhaji Bukar Abubakar, Zanna Dujiman Fika a matsayin Wakili na Musamman na Masarautar Fika. An haifi Alhaji Bukar Abubakar a garin Fika a ranar 20 ga  Afrilun 1945, ya kuma halarci Makarantar Alkur’ani a Fika. […]

Sarkin Fika ya nada Wakili na Musamman a masarautarsa

Alhaji Bukar Abubakar

Mai martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, ya tabbatar da nadin Alhaji Bukar Abubakar, Zanna Dujiman Fika a matsayin Wakili na Musamman na Masarautar Fika.

An haifi Alhaji Bukar Abubakar a garin Fika a ranar 20 ga  Afrilun 1945, ya kuma halarci Makarantar Alkur’ani a Fika.

Sai kuma Makarantar Elementary ta Potiskum sai babbar Makarantar Firamare ta Borno da Kwalejin Horar da Malamai ta Maiduguri da Babbar Kwalejin Horar da Malamai (Adbanced Teacher’s Collage), Kano daga nan sai ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Kafin nadin nasa shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar Kwalejin ’Yan Mata ta Tarayya (GGC) da ke Potiskum.

Marigayi Sarkin Fika Alhaji Abali Ibn Muhammad Idrissa ne ya nada Alhaji Bukar a matsayin Zannan Dujima,  kuma ya zama Shugaban Kwalejin Harkokin Mulki da Kasuwanci (CABS) da ke Potiskum, inda ya yi ritaya don kashin kansa a shekarar 2002 bayan ya shugabanci kwalejin na tsawon shekara15.

Nadin na Wakili ko Mataimaki na Musamman na Masarautar Fika yana kunshe ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun Sakataren Majalisar Masarautar Fika, Alhaji Muhammad Jalingo kuma nadin ya fara ne daga ranar 1 ga watan Yuni bana.