Sarkin Fika Ya Raba Wa Marayu Kudi da Kayan Sallah
Sarkin ya yi kira ga masu kishin al’umma da su rika taimaka wa marayu a kodayaushe domin samun ingantacciyar rayuwa.
Mai Martaba Sarkin Fika, Muhammadu Ibn Abali Muhammadu Idrissa ya bayar da tallafin kayan tufafi da kudi ga marayu da ke garin Potiskum domin bukukuwan Sallah.
Da yake raba kayayyakin a fadarsa da ke Potiskum, sarkin ya yi addu’ar samun hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar masarautar.
- Ya saci zakara saboda bai ci nama ba tun farkon Azumi
- Sallah: Yadda maza ke cin kasuwar yi wa mata kunshi da kwalliya a Kano
Sarkin ya yi kira ga masu kishin al’umma da su rika taimaka wa marayu a kodayaushe domin samun ingantacciyar rayuwa.
An zabo marayun ne daga gundumomin masarautar Fika baki daya.
A jawabinsa na godiya, Hakimin Arikime, Alhaji Haruna Usman, ya bayyana sarkin a matsayin shugaba abin koyi wanda a kodayaushe yake wa’azin zaman lafiya da tallafa wa marayu da marasa galihu a fadin masarautarsa.