Sarkin Fulani ya lashe amansa a ofishin ’yan sanda

Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu Abdulkadir Gaga, ya bayyana alhininsa kan kisan gillar Fulani makiyaya 13, a cikin watanni biyu, a sassa daban-daban na dajin yankin Oke-Ogun a Jihar Oyo ba tare da ’yan sanda sun kama kowa balle a gurfanar da su gaban kotu ba. Ya furta cewa, “Mun samu labarin wadanda aka kama […]

Sarkin Fulani ya lashe amansa a ofishin ’yan sanda

Sarkin Fulani Salihu Abdulkadir Gaga (a tsakiya) yayin da yake zantawa da ’yan jarida a garin IganganSarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu Abdulkadir Gaga, ya bayyana alhininsa kan kisan gillar Fulani makiyaya 13, a cikin watanni biyu, a sassa daban-daban na dajin yankin Oke-Ogun a Jihar Oyo ba tare da ’yan sanda sun kama kowa balle a gurfanar da su gaban kotu ba.
Ya furta cewa, “Mun samu labarin wadanda aka kama da hannu cikin wannan kisa, ana sallamarsu a cikin kwanaki biyu, ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba.” Sai dai yayin da ya ziyarci ofishin sashen manyan laifuka na rundunar ’yan sanda (CID) da ke Iyaganku a Ibadan, a ranar Litinin, kuma mataimakin kwamishinan ’yan sanda, AC Dasuki Galadanci ya yi masa bayani dalla-dalla na yawan mutanen da aka kama dangane da kashe-kashen kuma aka gurfanar da su gaban kotu da wadanda ake ci gaba da bincike kan su kafin a gurfanar da su, Sarkin Fulanin ya janye furucin nasa tare da yin nadama.
Sarkin Fulani Salihu, mai shekaru 68, shi ne shugaban kungiyar Jam Nati Fulbe (wato kungiyar Fulani masu samar da zama lafiya) na kasa baki daya, a zaman makoki da aka yi a fadarsa da ke garin Igangan, ranar Asabar, ya yi wa ’yan jarida bayanin matsalolinsu.
Ya ce, “A shekarun baya ba mu saba ganin irin wannan aika-aika ba. Muna zaune lafiya da al’ummar da ke wannan sashe na Oke-Ogun. Daga baya ne wannan masifa ta kunno kai, ake kashe mana mutane da sace dabbobinmu. Muna kira ga hukuma ta dauki matakin ba mu kariya saboda nan gaba. Dadewarmu a wannan sashe ya isa mu ci moriyar gwamnati. Hatta magungunan dabbobi da ake ba mu kyauta, yanzu ba ma samu.”
Sarkin Fulanin ya nuna gamsuwarsa da irin matakan ’yan sanda suka dauka na hanzarta binciken al’amarin kashe-kashen, musamman a yayin da ya ga takardun bayanan mutanen da aka gurfanar gaban kotu da wadanda ake ci gaba da bincike da kuma wadanda ake nema. Saboda haka ya jinjina wa Kwamishinan ’yan sanda Muhammed A. Indabawa kan lamarin.
Da yake yi wa Sarkin Fulanin bayani, AC Dasuki Galadanci ya bukaci a rika binciken al’amura kafin a yanke hukunci. “Muna maraba da zargi mai ma’ana da zai kai mu ga gudanar da ayyukanmu na tsaron lafiyar jama’a.” Inji shi.  
Tun farko a zaman makokin, shugaban kungiyar Jam Nati Fulbe, reshen Jihar Ogun, Alhaji Ibrahim Abubakar Dende, kira ya yi ga gwamnatocin tarayya da jihohi su samar da burtaloli ga Fulani domin kawo karshen fadace-fadacen da ake yi a tsakaninsu da manoma.
Ya ce, “Kodayake akwai irin namu laifi ko kuma kuskure da dabbobinmu suke shiga cikin gonakin manoma, amma mukan biya ramuwa ga manoman ba tare ma da hukuma ta tsoma baki ba. Wannan shi ne babban dalilin kafa wannan kungiya ta Jam Nati Fulbe, wacce ta dukufa wajen lalubo hanyoyin zama lafiya tsakanin Fulani da sauran al’ummomin kasa, musamman manoma, wadanda kan nemi a ba su ramuwar misalin Naira miliyan daya ga mai shanu guda goma da ya yi barna, lamarin da kan sa a jijiyar wuya a tsakani.”
Sarkin Fulanin Jihar Kogi, Alhaji Abubakar Dumile da Shugaban kungiya, Alhaji Musa Muhammed Jimoh da mataimakinsa, Alhaji Bami Fulba Abubakar da mataimakin sakatare, Alhaji Salihu Abdullahi Bwale suna daga cikin shugabannin Fulani da suka halarci zaman makokin.

…An kama miji da matarsa da zargin kashe Bafulatani

Kabir Yayo Ali, Daga Ibadan

Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta kama wani mutum mai suna Oderinde Joel da matarsa kan zargin kashe wani Bafulatani mai suna Aliu Abdullahi da yake kiwon shanu a dajin Iseyin yankin Oke-Ogun.
Mai gidan marigayin, Alhaji Abdullahi Audu da ke kauyen Okaka Sawo ne ya kai rahoton kisan a ofishin ’yan sanda na Iseyin, ya ce an harbe yaron ne da bindiga.
Babban jami’in ’yan sanda ya tura jami’ansa wurin da aka yi kisan, suka dauki gawar mamacin zuwa babban Asibitin Iseyin domin binciken dalilin mutuwarsa, kuma sun gano bindigar gargajiya da ake kyautata zaton da ita ce aka yi harbin da ya halaka shi.
Oderinde Joel da ake tsare da shi da matarsa bai musanta harbin da ya yi wa marigayin ba, sai dai ya ce ya aikata hakan ne a dalilin kururuwar neman ceto da matarsa ta yi a cikin gonar ta ce marigayi Aliu Abdullahi ya kama ta da karfi ya yi mata fyade.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Oyo, DSP Olabisi Ikobanafor ta tabbatar da aukuwar al’amarin, ta ce an tura wa sashen binciken manyan laifuka da ke Iyaganku a Ibadan domin ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu.