Sarkin Fulanin Oyo Zai Maka Sunday Igboho A Kotu
Basaraken ya ce maharan sun kona gidajensa da motoci da sauran kadarorinsa, banda shanunsa 207 da suka kora da kudinsu ya kai miliyan N500
Sarkin Fulanin Jihar Oyo, Alhaji Salihu Abdulkadir, wanda rikicin Igangan da taratsin kafa kasar Yarabawa, Sunday Igboho ya jagoranta ya tilasta tserewa da rayuwarsa, ya ce yana tunanin maka Igboho a kotu.
Rikincin Igangan da ya auku a 2021 ya tilasta basaraken barin Unguwarsa ta Ibarapa ta Arewa bayan Igboho da magoya bayansa sun kai msu farmaki tare da kona musu gidaje da dukiyoyi.
- Sabon fada ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a Ibadan
- Binciken kwakwaf: Su wane ne ’yan bindigar da suka addabi Zamfara?
Igboho da mabiyansa sun kai musu harin ne sati guda bayan ya bai wa Fulanin yankin wa’adin kwashe kayansu su bar Igangan, bisa zargin su da kai hare-hare.
Basaraken ya ce maharan sun kona gidajensa da motocinsa da sauran kadarorinsa, banda shanunsa 207 da suka kore gaba daya da kudinsu ya kai Naira miliyan 500.
Harin nasu Igboho ne ya sa dole sanya Sarkin Fulanin ya tattara iyalinsa suka koma da zama a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Ya bayyana wa Aminiya cewa su Igboho sun sanya shi cikin matsanancin talauci na ba gaira ba dalili, don haka dole ne a biya shi dukiyarsa da ya rasa sakamakon wancan hari da bai tsira da komai ba sai iyalinsa kawai.
Igboho dai na zargin Fulanin da far musu a Igangan, musamman ma harin da ya yi sandiyar mutuwar wani likita mai suna Fatai Aborode.