Sarkin Gassol ya bukaci gwamnati ta fara aikin noman zamani a yankinsa

Sarkin Gassol a Jihar Taraba, Alhaji Idi Ciroma ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Taraba su taimaka wajen soma gudanar da aikin noma na zamani a masarautarsa. Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Gassol inda ya ce akwai wani kamfani daga kasar waje wanda ya nuna sha’awar gudanar da noman shinkafa […]

Sarkin Gassol ya bukaci gwamnati ta fara aikin noman zamani a yankinsa
Sarkin Gassol ya bukaci gwamnati ta fara aikin noman zamani a yankinsa

Sarkin Gassol a Jihar Taraba, Alhaji Idi Ciroma ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Taraba su taimaka wajen soma gudanar da aikin noma na zamani a masarautarsa. Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Gassol inda ya ce akwai wani kamfani daga kasar waje wanda ya nuna sha’awar gudanar da noman shinkafa a masarautarsa amma har yanzu haka bai yiwu ba.

Sarkin ya nuna bukatarsa da ta jama’ar masarautar wajen ganin kamfanin ya fara gudanar noman shinkafa a yankin. Ya ce kamfanin wanda daga Amurka yake kuma yana da rassa a gabashin Afirka ya kai kayan aikin na biliyoyin Naira amma sabo rashin cika wasu ka’idoji a hukumance ya kasa fara gudanar da ayyukansa.
Alhaji Idi Ciroma ya ce masarautarsa da ke gefen kogin Binuwai na da albarkar kasar noma na rani da damina kuma tana iya samar da kashi 60 cikin 100 na shikafar da kasar nan take bukata.
Ya ce wannan ne ya sa tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da hadin gwiwar Gwamnatin Taraba suka kawo kamfanin domin gudanar da noman shinkafa da sarrafa ta. Sarkin ya ce manoman yankin wadanda suka hada da shi kansa suna noma shinkafa da masara mai yawan gaske a duk shekara amma saboda rashin taimakon kayan aiki da takin zamani da kasuwa mai kyau ya sa suna fuskantar asara a mafi yawan lokuta.
Ya ce wata matsala wanda ke gallabar manoman yankin ita ce ta wata ciyawa da manoman suka sa wa suna Boko Haram, ya ce duk inda wannan ciyawa ta bulla manoma na tafka asaran amfanin gonarsu.
Sarkin ya ce akwai gonar da yake noma buhu dubu uku na shikafa kafin bullar wannan ciyawa amma da ta bulla da kyar ya samu buhu dubu da dari uku. “Wannan ciyawa da ake kira Boko Haram ta kawo babbar matasla ga noman shinkafa a masarautata da sauran yankunan da ake noman shinkafa a Jihar Taraba,” inji shi.
Ya bukaci Ma’aikatar Gona ta Tarayya da ta jihar su gudanar da bincike a kan wannan muguwar ciyawa don kawo karshen illar da take yi wa shinkafa a jihar