Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ya rasu
Sarkin Fadar Gaya, Alhaji Bashir Gaya, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Gaya.
Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ya riga mu gidan gaskiya.
Masarautar Gaya ta tabbatar da rasuwar basaraken ne a safiyar Laraba, ta bakin Sarkin Fadar Gaya, Alhaji Bashir Gaya.
- ’Yan bindiga daga Zamfara da Katsina sun fara kai hari Kano
- A bude wa ’yan bindiga wuta ko sun shiga cikin mutane —Masari
Masautar Gaya na daga cikin sabbin masarautu hudu da aka kirkiro a Jihar Kano a shekarar 2019.
Kafin daga likafarsa zuwa Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, shi ne Hakimin Kunci.
An bayar da rahoton rasuwar Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya. Sarkin ya rasu da sanyin safiyar Laraba bayan rashin lafiya na tsawon shekaru.
Da yake tabbatar da rasuwar, Ajiyan Gaya Malam Shamsu Isa Kademi ya ce Marigayi Sarkin Gaya ya rasu bayan fama da rashin lafiya yana da shekara 91 a duniya.
Ya kasance a kan karagar mulki tun bayan nadin sa a matsayin Hakimin Sarkin Gaya a 1990.
Ya kuma rike mukaman gargajiya da dama kamar Hakimin Kunchi, Hakimin Minjibir da sauransu.