Sarkin Gbagyi ya zama mai daraja ta daya

Gwmnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya daukaka martabar Sarkin Gbagyi (Esu Chikun) Dokta Danjuma Barde daga daraja ta biyu zuwa sarkin mai daraja ta daya. An nada Sarkin a sarautar Sa Gbagyi ne a ranar 29 ga watan Disambar 2000 wanda yanzu ake kira da Esu Chikun bayan Gwamnan El-Rufai ya sauya fasalin […]

Sarkin Gbagyi ya zama mai daraja ta daya

Gwamna Kaduna Nasir El-Rufai

Gwmnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya daukaka martabar Sarkin Gbagyi (Esu Chikun) Dokta Danjuma Barde daga daraja ta biyu zuwa sarkin mai daraja ta daya.

An nada Sarkin a sarautar Sa Gbagyi ne a ranar 29 ga watan Disambar 2000 wanda yanzu ake kira da Esu Chikun bayan Gwamnan El-Rufai ya sauya fasalin masarautu, inda aka canja sunayen masarautun daga sunayen kabilu zuwa na garuruwa.

Ya hau kan karagar sarautar a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2001 a matsayin Sarki mai daraja ta uku. Shekara shida bayan nan, a shekarar 2007 aka sake daukaka darajar masarautar zuwa sarki mai daraja ta biyu kafin a wannan shekarar kuma gwamnan Jihar Kaduna ya amince da kara masa girma zuwa Sarki mai daraja ta daya, kamar yadda yake kunshe cikin takardar sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai, Samuel Aruwan ya sanyawa hannu.

Gwamnan, ya bayyana a cikin takardar cewa Esun na Chikun, Dokta Barde, ya cancanci wannan matsayin ne saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya bayan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Kaduna karkashin shugabancin Farfesa Kabir Mato ta ba da shawara.

“Irin kokarin da yake nuna wa wajen samar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin kabilun da ke zaune a masarautarsa ce wanda har gwamnatin jihar ta lura da haka kuma har ta rubuta masa takarda kan hakan.”

Farfesa Mato ya ce lura da aka yi da kasancewar masarautarsa ta kunshi garuruwan da ke cikin kwaryar Kaduna ta janyo hankalinsu wajen daukaka wannan masarautar domin ba shi karin dama da kwarin gwiwar ci gaba da gudanar da ayyukansa inda aka hada masa da yankin karamar hukumar Chikun gaba daya a karkashin masarautarsa. Esu Chikun, Dokta Danjuma Barde ya yi karatunsa na digiri ne a harkokin Ilmi (Education) inda ya yi aiki a matsayin malami. Sannan ya taba zama wakili a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna.