Sarkin Gombe ya jinjina wa Sarkin Gwandu

Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya yaba wa Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kebbi Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar kan kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kebbi.Alhaji Abubakar Shehu ya yi yabon ne lokacin da ya kai wa Sarkin Gwandun ziyarar ban girma a fadarsa a Birnin Kebbi.Sarkin […]

Sarkin Gombe ya jinjina wa Sarkin Gwandu
Sarkin Gombe ya jinjina wa Sarkin Gwandu

Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya yaba wa Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kebbi Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar kan kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kebbi.
Alhaji Abubakar Shehu ya yi yabon ne lokacin da ya kai wa Sarkin Gwandun ziyarar ban girma a fadarsa a Birnin Kebbi.
Sarkin ya ce ba a Jihar Kebbi kadai Sarkin Gwandu yake ba da gudunmawar zaman lafiya ba har da Najeriya, kasancewarsa daya daga cikin gogaggun shugabanni masu hangen nesa.
Da yake maida jawabi, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya ce, ya ji dadin ziyarar da Sarkin Gombe ya kai a fadarsa, inda ya ba shi shawarar ya yi ta hakuri da jama’ar da Allah Ya dora masa ya shugabanta domin yanzu ya zama uban kowa.