Sarkin Gombe zai nada Gwamna Inuwa Yahaya sarauta
Sarkin na Gombe zai nada Gwamna Inuwa Yahaya ne sarauta Dan Majen Gidan Bubayero.
Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na III ya aike da wata tawaga don sanar da Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya game da sarauta Dan Majen Gidan Bubayero da za a nada shi.
Tawagar dai ta fadar gwamnatin Jihar ne ranar Lahadi, karkashin jagorancin Walin Bauchi, kuma tsohon gwamnan Jihar ta Bauchi, Ahmad Adamu Mu’azu.
- ’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a sansanin sojoji a Sakkwato
- Saniyar da ta fi kankanta a duniya ta mutu
A jawabinsa a madadin tawagar, Sallaman Sarkin Gombe, Usman Adamu Barde, ya ce Mai Martaba ya aiko su ne da sako su gaya masa ya ba shi Dan Majen Gidan Bubayero.
Ya ce cancantar Gwamnan tasa Sarkin ya ga dacewar ba shi sarautar.
Shi ma ya ke jawabin maraba, jagoran tafiyar, Ahmad Adamu Mu’azu, ya ce Sarkin ya sa shi ya jagoranci tawagar ne saboda alakar dake tsakanin Bauchi da Gombe mai dadadden tarihi.
Ya ce koda dai wasu za su ga lamarin kamar na siyasa, amma ba haka ba ne.
Da yake mayar da jawabin godiya a madadin iyalan Marigayi Yahaya Umaru, Baffan Gwamnan Alhaji Muhammad Bello Umar, wanda tsohon Darakta ne a hukumar NDIC godewa Sarkin ya yi bisa wannan karamci da ya yiwa dansu.
Mohammad Bello Umar, ya kuma ce tun suna kanana sun tashi sunga kakannin su suna da alaka da fadar Gombe, kuma har yanzu ba ta yanke ba.
“Ko lokacin rasuwar marigayi Alhaji Umaru Tsoho, Sarki Abubakar ne ya yi masa sallar jana’iza,” inji shi.
Kazalika, ya ce lokacin fafutukar neman jihar Gombe ma, Alhaji Yahaya Umar, mahaifin Gwamnan ya taka muhimmiyar rawar har aka sami nasara.