Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu

Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.

Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis.

Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.

Sakataren masarautar Gudi da ke Gadaka ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya kuma ce an shirya gudanar da Sallar Jana’izar marigayi Sarkin a ranar Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Sarkin da ke Gadaka.

Labarin rasuwar Sarkin dai ya tayar da hankalin a ɗaukacin al’ummar masarautar da ma Jihar Yobe baki ɗaya, inda da yawa ke jinjinawa jagorancinsa da kuma abin da ya bari.

Ana ci gaba da miƙa saƙon ta’aziyyarsu daga ko’ina, a dai-dai lokacin da jama’a ke juyayin rashin Sarkin.

Marigayi Sarkin Gudi ya shahara wajen hikima da jagoranci da jajircewa wajen ci gaban al’ummarsa tare da  taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da haɗin kai a tsakanin al’umma, kuma za a riƙa tunawa da abin da ya bari har zuwa tsawan lokaci.

Sallar jana’izar wadda manyan malamai za su jagoranta, za ta samu halartar manyan baƙi, shugabannin gargajiya da sauran al’umma.

Za a binne gawar Sarkin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin na Gadaka.

Al’ummar masarautar dai na cikin alhini, inda da dama ke nuna alhininsu dangane da rashin jagoransu.

Ana sa ran gwamnati da al’ummar Jihar Yobe za su yi wa marigayi Sarkin gaisuwar ban girma, ganin irin rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.