Sarkin Gwandu na nan da ransa – Fadar Sarki
Fadar mai martaba Sarkin Gwandu ta karyata labarin da wasu kafafen watsa labarai suka bayyana na cewa mai Sarki Muammad Ilyasu Bashar ya rasu. A wata takarda da aka raba wa manema labarai a fadar, mai dauke da sa hannun Sakataren Sarkin, Musa Usman Bashar, ta yi nuni da cewa wannan labari ba gaskiya ba […]
Fadar mai martaba Sarkin Gwandu ta karyata labarin da wasu kafafen watsa labarai suka bayyana na cewa mai Sarki Muammad Ilyasu Bashar ya rasu.
A wata takarda da aka raba wa manema labarai a fadar, mai dauke da sa hannun Sakataren Sarkin, Musa Usman Bashar, ta yi nuni da cewa wannan labari ba gaskiya ba ne, ba shi da tushe ballantana makama. Saboda haka ana shaida wa dukkan jama’ar kasar nan cewa mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo-Janar Muhammad Ilyasu Bashar (ritaya) yana cikin koshin lafiya kuma yana gudanar da ayyukansa kamar yadda ya saba.
Takardar ta ci gaba da cewa fadar sarkin tana godiya ga dukkan jama’a da suka nuna damuwa da kuma kulawa dangane da abin da ya faru, kuma ta yi kira ga kafafen watsa labarai na cikin gida da na waje, da su dinga tantance labari na gaskiya kafin su yada shi ga duniya, domin kauce wa fitina a cikin al’umma.