Sarkin Gwandu ya shawarci Gwamnatin Kebbi kan ilimi

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya bukaci Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa kwamitin gaggawa don magance matsalolin da ilimi ke fuskanta a jihar. Sarkin ya ba da wannan shawara ce a yayin da yake jawabi ga iyayen kasa da hakinmai a fadarsa ta Abdullahi Fodiyo da ke a Birnin-Kebbi wurin gudanar da […]

Sarkin Gwandu ya shawarci Gwamnatin Kebbi kan ilimi

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya bukaci Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa kwamitin gaggawa don magance matsalolin da ilimi ke fuskanta a jihar.

Sarkin ya ba da wannan shawara ce a yayin da yake jawabi ga iyayen kasa da hakinmai a fadarsa ta Abdullahi Fodiyo da ke a Birnin-Kebbi wurin gudanar da addu’o’in mako-mako da ake yi  duk ranar Juma’a a fadar domin neman zaman lafiya ga jihar da kasa bakin daya.

Sarkin ya ci gaba da cewa kwamitin da gwamnati za ta hada ya zamana cewa zai magance cinkoson dalibai a ajujuwan makarantun firamare da sakandaren  jihar.

Haka kuma ya ce “Duk malaman da za a dauka don su karantar a tabbatar da cewa sun san aikin karantarwa kafin a dauke su aikin Gwamnatin Kebbi ta yi iya kokarinta a fannin gine-gine da gyaran makarantun firamare da na sakandare da kuma ba da  horo da horarwa ga malamai a jihar. Kuma akwai bukatar malaman su saka wa gwamnatin jihar kan wadannan abubuwan da ta yi ta hanyar yin aikinsu na karantarwa kamar yadda dokar aikin ta tanada.”

Sarkin ya yi kira ga jami’an Ma’aikatar Ilimi ta Jihar su tabbatar da cewa ana sanya ido sosai kan malaman makarantu a jihar don a samu ingantaccen aiki da kuma karantarwa ga dalibai. Kuma ya gargadi malaman kwalejoji da kuma na jami’ar jihar su daina ba da makin jarrabawa kyauta ga daliban da suka fadi a jarrabawa, saboda yana kawo nakasu da kuma koma baya ga harkar ilimi a jihar da kasa bakin daya.