Sarkin Hausawa ya koka kan yadda ’yan Arewa ke guje wa karbar katin zabe
Sarkin Hausawan Iperu-Remo, a Jihar Ogun, Alhaji Mustapha Dikko, ya nuna takaicin ganin yadda al’ummar Arewacin kasa suke yin sako-sako da karbar katunan zabe a rumfunan da Hukumar zabe (INEC) ta tanada, domin yin rajistar sunaye da mika katunan dindindin ga jama’a, da za su yi amfani da su wajen zaben ‘yan takarar da suke […]
Sarkin Hausawan Iperu-Remo, a Jihar Ogun, Alhaji Mustapha Dikko, ya nuna takaicin ganin yadda al’ummar Arewacin kasa suke yin sako-sako da karbar katunan zabe a rumfunan da Hukumar zabe (INEC) ta tanada, domin yin rajistar sunaye da mika katunan dindindin ga jama’a, da za su yi amfani da su wajen zaben ‘yan takarar da suke so a zaben badi.
Alhaji Mustapha Dikko, ya ce, “hakika muna fama da jan aiki a game da wannan al’amari da mutanenmu suke dari dari da kin jure wa zafin rana domin tsayawa a yi musu rajistar sunaye da mika musu katin zabe. Mun nemi malamai da limamai su hanzarta fadakar da mutane a cikin makarantu da masallatai a game da muhimmancin karbar katin zabe, wanda shi ne makami gare mu. Amma, abin kunya shi ne, irin yadda sauran kabilu suke tsayawa cikin ruwa da rana suna bin dogayen layi domin neman ‘yancin su, sai ga shi mutanenmu suna yin ko oho, duk kuwa da fadakarwar da muka dade muna yi musu a kan amfanin katin gare su.”
Sarkin Hausawan wanda yake fadin haka cikin hira da wakilinmu a fadarsa da ke garin Iperu-Remo, bayan dawowa daga ziyarar rumfunan zabe, domin gane wa idanunsa irin yadda ake yin rajistar sunayen mutane a rumfunan zabe na masarautarsa, a ranar Juma’a da ta wuce,
“daya daga cikin matakan da muka fara dauka a matsayinmu na shugabanni, shi ne, ziyarar unguwanni da muka rinka yi a wannan rana domin yekuwa da tabbatar da ganin mutanenmu maza da mata sun fito yin rajistar sunaye da karbar katunan zabe, domin yin hakan ne zai bas u ‘yancinsu a nan gaba idan Allah ya yarda,” inji shi.
Dangane da matsayin mahukumta a kan wannan al’amari, sai Sarkin Hausawan ya ya ce, “a hakikanin gaskiya babu wata alamar kabilanci da Gwamnatin Jihar Ogun, take nuna mana a kan wannan al’amari. A maimakon haka ma, sun yi ta aiko wakilansu ne domin wayar da kan mutanenmu a game da muhimmancin fitowa domin karbar katin amma, abin bakin ciki, sai ka ga mutanen mu sun kasa yin juriya a cikin ruwa da rana da dogayen layi domin karbar katunan. Wannan ita ce babbar matsalar da muke fuskanta.”
“Saboda haka ina yin kira da kakkausan harshe ga dukkan al’ummar Arewacin kasa mazauna wannan sashe su gane cewa, karbar wannan kati shi kadai ne damar samun ‘yancinmu a tafin hannunmu. Ya zame mana dole mu jajirce tamkar wani fito na fito na kalubalen rayuwa ne. Abin kunya ne gare mu ganin cewa, sashen Arewacin Najeriya shi ne da yawan mutane amma, har yanzu mun kasa yin amfani da wannan dama wajen jajircewa domin cimma buri. Idan muka bari wannan dama ta subuce mana to, mu kuka da kanmu,” a cewar Sarkin Hausawan Iperu-Remo, OlfijahlA Mustapha Dikko.