Sarkin Hausawan Agbor ya shawarci matasa
Sarkin Hausawan garin Agbor a Jihar Delta, Alhaji Umaru Hasan ya bayyana bukatar da ke akwai tare da shawartar matasa su mayar da hankali wajen rungumar neman ilimi da guje wa shaye-shayen ababen sa maye da wasu daga cikinsu suke amfani da su, musamman a lokacin hargowar tarukan siyasa da sauran irinsu a kasar nan.Alhaji […]
Sarkin Hausawan garin Agbor a Jihar Delta, Alhaji Umaru Hasan ya bayyana bukatar da ke akwai tare da shawartar matasa su mayar da hankali wajen rungumar neman ilimi da guje wa shaye-shayen ababen sa maye da wasu daga cikinsu suke amfani da su, musamman a lokacin hargowar tarukan siyasa da sauran irinsu a kasar nan.
Alhaji Umaru ya yi furucin hakan ne a lokacin wata zantawarsa da Aminiya a fadarsa da ke garin Agbor, inda ya yi nunin cewa, “Babu abin da ya gurbata tarbiyyar matasa a kasar nan irin jahilci na rashin ilimin addini da na zamani, sannan da uwa uba, lamarin da ke sanyawa su fada wa irin shan kayan maye, inda wasunsu suka maida shi tamkar addini cikin rayuwarsu. Don haka kiran da nake yi wa matasanmu da shawarar da nake ba su shi ne su bar wannan dabi’a ta shaye-shaye, su koma makaranta su nemi ilimi. Muddin sun samu ilimi, to lallai zai buda musu hanyar alheri, wadda za su samu su amfani kansu da kasa baki daya”.
Daga nan kuma sai Sarkin Hausawan ya ja hankalin al’ummar Arewa mazauna garin Agbor da ma jihar ta Delta baki daya da su tattali yin hakuri cikin al’amurransu na rayuwa, su rungumi juna, su hada kai, su fuskanci neman arziki da ya kawo su yankin Kudu. “Shawarata ga al’ummar Hausawa mazauna garin Agbor da kewayenta ita ce su kasance masu hakuri da juna da kuma sauran kabilun yankin da suke zamantakewa da su domin a cigaba da samun dorewar zaman lafiyar da muke da ita a halin yanzu a nan garin da yankin Kudu baki daya”. Inji shi.
A karshe Sarkin sai ya yi wa Najeriya addu’ar fatar alheri da zaman lafiya, musamman yankin Arewa da al’ummarta suke fuskantar fargabar masu tayar da kayar baya a wasu sassa na yankin. Ya bukaci Allah Ya ba da zaman lafiya mai dorewa a gaba dayan Najeriya.