Sarkin Hausawan Ijora ya nemi sarakunan Hausawa su hada kansu

Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun (masarautar Ojora) a Jihar Legas, Alhaji Adamu Abubakar Naby ya ce, “Muddin sarakunan Hausawa suka kasa hada kawunansu domin tafiya da murya daya to kuwa za a bar al’ummarsu a baya ta fannin cin moriyar abubuwan ci gaban rayuwa da Gwamnatin Jihar ta saba yi wa al’ummomi. Yau fiye da shekaru […]

Sarkin Hausawan Ijora ya nemi sarakunan Hausawa su hada kansu
Sarkin Hausawan Ijora ya nemi sarakunan Hausawa su hada kansu

Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun (masarautar Ojora) a Jihar Legas, Alhaji Adamu Abubakar Naby ya ce, “Muddin sarakunan Hausawa suka kasa hada kawunansu domin tafiya da murya daya to kuwa za a bar al’ummarsu a baya ta fannin cin moriyar abubuwan ci gaban rayuwa da Gwamnatin Jihar ta saba yi wa al’ummomi. Yau fiye da shekaru 100 Hausawa ke zaune a Legas kuma suke bayar da gudunmawarsu ga bunkasar tattalin arzikin jihar ta hanyar safarar kayan abinci da dabbobi daga Arewa amma, sai aka bar mu a baya a dalilin rashin hadin kan shugabanninmu. Mahukunta a Legas sun kasa janyo shugabanninmu a jiki kamar yadda ake yi wa wasu kabilu ne saboda mun kasa hada kanmu.”

Ya ci gaba da cewa: “Duk da yake mafi yawancin Sarakunan Hausawa da suka yi mulki a baya a garuruwa daban-daban na jihohin Kudu sun aza mana tubalin ginin rayuwa bisa irin hikima da dabarunsu da suka cancanci a jinjina masu amma yanzu zamani ya canza, akwai bukatar samun shugabanni masu ilmin addini da na zamani da jin yaren mutanen gari domin samun saukin tafiyar da al’amura da fahimtar juna.”
Ya ce bayan rasuwar Sarkin Hausawa, Onuh na Igala na Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Akoh dangara, sai shugabannin kabilun Arewa da jama’arsu baki daya suka amince da nada shii a matsayin jagoransu a wannan masarauta, wanda Mai martaba Ojora na masarautar Ijora Oba Fatai Aremu Oyeyinka Aromire ya tabbatar da nadin da mika masa satifiket a gaban jama’a. Daga cikin shugabanni wadanda ba ’yan asalin Jihar Legas ba ne, shi kadai aka sanya a cikin Hakimai da suke wakiltar masarautar Ojora.
“Ayyukan da na yi a matsayin sojan ruwa a karkashin gwamnoni da ministoci da wasu rundunonin tsaro na kasa a zamanin mulkin farar hula da soja sun ba ni damar ziyarar sassa daban-daban a Najeriya da wasu kasashen duniya da na halarci kwasa-kwasai, na samu gogewa a kan dabarun yaki da zamantakewar jama’a da mahukunta domin samun zama lafiya da kwanciyar hankali. Wannan damar nake son yin amfani da ita domin lalubo hanyar da zan bayar da gudunmawar ci gaban ’yan Arewa mazauna wannan sashe musamman da yake na waye da Legas da jin yaren jama’arsu. Amma hakan ba zai samu ba sai mun samu kyakkyawan hadin kai a tsakanin shugabanninmu domin tafiya da murya daya da zai kai ga cin ma burinmu.”