Sarkin Hausawan Ilori ya jinjina wa Buhari a kan tsaro

Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawan Jihar Kwara, Sarkin Hausawan Ilori, Alhaji Abubakar Ibrahim, ya nemi Sarakuna da Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni da Shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa da matasa da direbobin motocin sufuri musamman a Arewacin kasa da, su fito da sabon salon zamantakewa mai dorewa a tsakanin al’ummomi daban daban ba tare da kyamar […]

Sarkin Hausawan Ilori ya jinjina wa Buhari a kan tsaro
Sarkin Hausawan Ilori ya jinjina wa Buhari a kan tsaro

Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawan Jihar Kwara, Sarkin Hausawan Ilori, Alhaji Abubakar Ibrahim, ya nemi Sarakuna da Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni da Shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa da matasa da direbobin motocin sufuri musamman a Arewacin kasa da, su fito da sabon salon zamantakewa mai dorewa a tsakanin al’ummomi daban daban ba tare da kyamar juna da yake haifar da rabuwar kawunan jama’a ba.
“Su kuma ‘yan siyasa, kamata yayi suyi koyi da shugabannin baya tsakaninsu da Allah wajen shimfida siyasar kishin kasa ba siyasar kishin kai bad a wariya.” inji shi.
Sarkin ya yi wannan tsokaci yayin da yake jawabi ga Sarakunan Hausawan Jihar Kwara da manyan malamai da suka taru a fadarsa dake Zango Ilori, domin yin addu’o’i na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdulfatah Ahmad na jihar Kwara da zababbun ‘yan majalisu na jihar da Uban tafiya mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Sulu Gambari.
“Babban nauyi ne a kan shugabannin al’umma su sadaukar da kawunansu da dukiyarsu wajen tabbatar da ganin sun hada kawunan jama’arsu da samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu. Hakan zai samu ne idan dukkanmu shugabanni da talakawa mun nuna kishin kasar haihuwarmu kamar yadda wasu kasashen duniya suka yi, da ya kaisu ga ci gaba. Bai kamata mu rinka koyawa ’ya’yanmu dabi’ar banbancin kabila da addini ba domin yin haka ne zai haifar da samun shugabanni marasa kishin kasa a nan gaba. Kuma hakan ne zai haifar da tafiyar hawainiya da ake samu ga ci gaban Najeriya,” inji Sarkin Hausawan na Ilori.
Dangane da matsalar tsaro, Sarkin Hausawan kuma ya jinjina wa matakin farko da sabuwar gwamnati a karkashin jagorancin Shugaba Buhari, ta dauka a kan nuna damuwarta a kan wannan al’amari ne. Ya ce, “a daidai lokacin da mahukumta suke gudanar da irin na su aiki a kan tsaron lafiyar kasa da al’ummarta, mu kuma jama’a kamata yayi mu bayar da irin tamu gudunmawa tsakani da Allah wajen hakuri da jajircewa musamman ta fannin sanya ido da kyakkyawan lura da irin mutanen da muke cakuda da juna a cikin masallatai da majami’u da kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a domin bankado miyagun iri da mika su ga jami’an tsaro.”
Da yake Magana a kan matsalar jayayyar shugabanci da ya dabaibaye wasu shugabannin Hausawa a Jihar Kwara, Sarkin ya nuna matukar farin ciki da samun fahimtar juna a tsakanin wadannan al’umma a zamanin mulkinsa na shekaru biyu.