Sarkin Hausawan Jattu ya nemi a zauna lafiya
Alhaji Ishaku Bako Garba, Sarkin Hausawa Jattu a karamar Hukumar Etsako ta yamma cikin Jihar Edo ya bayyana bukatar da ke akwai na kara karfafa dankon zumunci da hada kai da juna tsakanin al’ummar Arewa da ’yan asalin Jihar Edo. Ya bayyana bukatar hakan kuma ya yi kira ga daukacin ’yan Arewa mazauna Jihar Edo […]
Alhaji Ishaku Bako Garba, Sarkin Hausawa Jattu a karamar Hukumar Etsako ta yamma cikin Jihar Edo ya bayyana bukatar da ke akwai na kara karfafa dankon zumunci da hada kai da juna tsakanin al’ummar Arewa da ’yan asalin Jihar Edo.
Ya bayyana bukatar hakan kuma ya yi kira ga daukacin ’yan Arewa mazauna Jihar Edo a wata zantawarsa da Aminiya a fadarsa da ke garin Jattu a karshen makon jiya. Ya ce: “A hakikanin gaskiya mu ’yan Arewa mazauna nan karamar Hukumar Etsako ta yamma da sauran ’yan uwanmu da suke zaune cikin sauran kananan hukumomin nan guda 18 na Jihar Edo, muna zaman lafiya; don haka akwai bukatar mu kara hada kanmu domin samun ci gaba da dorewar zaman lafiya.”
Daga nan kuma sai ya kara da cewa: “Kowa ya san wannan jihar da zaman lafiya, domin ko a can baya lokacin yakin basasa, mutanen Edo sun taimaka wa ’yan Arewa ba kadan ba, don haka ina kira ga daukacin ’yan Arewa mazauna jihar da su guji bin duk wata hanya da za ta jawo fitina saboda siyasa ko addini, domin zan yi misali da Jihar Edo yadda al’umma suka dauki ’yan Arewa tamkar ciki daya ya haife su; dalilin wannan kaunar ta sa har sun yarda muna auratayya tsakanin jun.”
Ya karkare da kiran ’yan uwansa sarakuna da cewa su hada kai kuma su rike gaskiya, su ci gaba da yi wa kasar nan da shugabanninta adduo’i na fatan alheri, domin samun dorewar zaman lafiya.